Jaipur: Tsawa ta kashe mutum 16 suna cikin ɗaukar hoto a Indiya

Asalin hoton, NurPhoto
Tsawa ta kashe a ƙalla mutum 16 tare da jikkata wasu da dama a garin Jaipur da ke arewacin Indiya a ranar Lahadi.
Mutanen suna ɗaukar hoton "selfie" ne a cikin ruwan da ake sheƙawa a saman wata hasumiya da ke wani gini mai tarihi na yawon buɗe ido.
Mutum 27 ne ke kan ginin da kuma bangon a lokacin da abin ya faru, kuma rahotanni sun ce wasu daga cikin su sun yi tsalle sun faɗa ƙasa.
A ƙalla mutum 2,000 tsawa ke kashewa duk shekara a Indiya.
Wani babban jami'in ɗan sanda ya shaida wa kafafen yaɗa labarai cewa mafi yawan mutanen da suka rasun matasa ne.
A ranar Lahadi kaɗai an samu rahotannin mutuwar mutum tara a faɗin jihar Rajasthan inda Jaipur yake, a cewar kafofin yada labaran yankin.
Rahotanni sun ce ana kuma samun rahotannin mutuwa a sauran jihohi sakamakon faɗuwar tsawa.
An ruwaito cewa a ƙalla mutum 41 - mafi yawa mata da yara ne tsawa ta kashe a gundmomin jihar Uttar Pradesh. Mafi yawan waɗanda suka rasun mutum 14 a birnin Prayagraj suke.
Manyan ministocin Uttar Pradesh da Rajasthan sun sanar da biyan dala 6,700 a matsayin diyya ga iyalan waɗanda suka rasun.
Ofishin Firaminista Narendra Modi ma ya sanar da biyan dala 2,681 ga iyalan mamatan a dukkan jihohin uku.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Damuna na farawa ne daga watan Yuni zuwa Satumba a kowace shekara, inda ake zabga ruwan sama.
Hukumar Kula da Yanayi ta Indiya ta ce mace-mace sakamakon faɗuwar tsawa ya nunka a Indiya tun bayan shekarun 1960 - kuma sun ce ɗaya daga cikin dalilan shi ne sauyin yanayi.
Bayanan sun ce faɗuwar tsawa ta ƙaru da kashi 30 zuwa 40 cikin 100 a wuraren tsakiyar shekarun 1990.
A shekarar 2018, an yi tsawa sau 36,749 a jihar Andhra Pradesh da ke kudancin ƙasar kaɗai cikin sa'a 13 kacal.
Jami'ai sun ce an fi samun hakan a yankunan da ba su da bishiyoyi masu duhuwa, inda hakan ke jawo mutane ke zama cikin tsautsayin tsawar ta faɗa musu.
Abin da za ku yi don kauce wa faɗuwar tsawa
- Ku nemi mafaka a babban gini ko cikin mota
- Kar ku yi mafaka a fili fetal da kuma saman ginin
- Idan ba ku da wajen ɓuya, to ku zauna ku haɗe ƙafafunku waje ɗaya, tare d asaka kanku cikin gwiwowinku sannan ku sa hannunku ku riƙe kan da shi..
- Kar ku samu mafaka a ƙarƙashin bishiya.











