Abduljabbar Kabara: Abin da ya sa Sheikh Saleh Pakistan ya kai ƙarar Sheikh Abduljabbar

Kiyawa

Asalin hoton, Kano Police Command

Bayanan hoto, DSP Kiyawa ya ce har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike
An wallafa

Rundunar ƴan sanda jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta gayyaci Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya bayyana a gabanta a ranar Litinin 12 ga watan Yuli don amsa wasu tambayoyi kan ƙararsa da wani malamin ya kai.

Hakan na zuwa ne kwana biyu bayan kammala muƙabala tsakanin Sheikh Abduljabbar da wasu Malaman Kano.

Sai dai kakakin ƴan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce gayyatar da suka yi wa Malam Abduljabbar Nasir Kabara ba ta da alaƙa da muƙabalar da aka yi da shi ko kalaman da malaman jihar ke zargin sa da yi.

"Wannan gayyata ba ta da alaƙa da wannan zama da aka yi, dama tun kafin a yi wannan zama akwai waɗanda suka shigar da ƙorafe-ƙorafe a kansa, kuma an fara bincikawa, in ji Kiyawa.

DSP Kiyawa ya ce har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike.

"Dama an sa ranar dawowa don ci gaba da binciken, to kuma yau ce ranar kamar yadda aka sa a baya," ya ƙara da cewa.

Wa ya kai ƙarar Malam Abduljabbar?

Shugaban ƙungiyar Izala na Kano Sheikh Saleh Pakistan ne ya kai koke wajen ƴan sanda kan zargin cewa Malam Abduljabbar na barazana ga rayuwarsa.

Ya shigar da koken ne a watan Fabrairu, kuma tun daga wancan lokaci Malam Abduljabbar kan je wajen ƴan sanda lokaci zuwa lokaci.

Gayyatar ta wannan karo ta zo ne tun ranar a Juma'a jajiberin muƙalabala, amma Malam Kabara ya nemi uzuri cewa ga abin da ke gabansa yana kuma aikin haɗa littattafai, amma ya yi alƙawarin zai kai kansa a ranar Litinin.

Sheikh Pakistan ya shaida wa BBC Hausa cewa wannan barazana da Malam Abduljabbar ya yi masa ta kai shekara guda.

"Wani saƙo na ji yana yawo a shafukan sada zumunta inda yake cewa a kashe ni, kuma har wasu muƙarabbansa na tuntuɓa sun kuma tabbatar min da hakan cewa a gabansu ma ya yi batun.

Sheikh Saleh Pakistan

Asalin hoton, Prof Saleh Pakistan Facebook

Bayanan hoto, Sheikh ya shigar da koken ne a watan Fabrairu kan zarhin Malam Abduljabbar da yi wa rayuwarsa barazana

Da BBC ta tambaye shi ko me ya sa ya yarda cewa da shi Sheikh Abduljabbar yake, sai Malam Saleh Pakistan ya ce, "Sunana fa yake kamawa ɓalo-ɓalo."

Malamin ya ƙara da cewa: "Da ban yi niyyar kai ƙara ba, saboda ya yi wa Annabi SAW ma balle ni.

"Amma sai ƙwararru suka ba ni shawara cewa gara na kai ƙara saboda akwai bambanci, wannan abu ne da ya shafi rayuwa da mutuwa," a cewarsa.

Ya ce tun farko kotu ya kai wa ƙorafi sai ita kuma ta tura wa ƴan sanda da zummar idan sun kammala bincike za a mai da lamarin kotu.

"To da alƙalai suka shiga yajin aiki sai maganar ta kwanta sai yanzu da suka taso ta dawo. Na san idan sun kammala jin ta bakinsa ni ma za a gayya ce ni," in ji shi.

BBC Hausa ta sake tambayar Sheikh Saleh Pakistan ko ya tuntuɓi Sheikh Abdukjabbar kafin kai shi ƙarar? Sai ya ce: "Ban tuntuɓe shi ba saboda yadda ya ɗauki tsarinsa na ashar da cin mutunci."

Kwana ɗaya bayan kammala muhawarar malaman dai Sheikh Abduljabbar ya nemi afuwar al'ummar Musulmai har sau biyu a ranar Lahadi, kan ɓatancin da ake zarginsa da yi wa Manzon Allah SAW, wanda ko a lokacin neman afuwar ya sake jaddada cewa ba ya yi wa Ma'aiki ɓatanci.

Sai dai Malam Saleh Pakistan ya ce wannan neman afuwa ba ta shafi tasu shari'ar ba, "Haƙurinsa ba a kan shari'armu ba ne, ba huruminmu ba ne.

"Ba zan ce komai ba har sai abin da kotu ta ce don ba a magana kan batun da ke gaban kotu," in ji shi.

BBC ta yi ta ƙoƙarin jin ta bakin Sheikh Abduljabbar amma wayarsa ba ta shiga. Sai dai za mu ƙara bayanan abin da ya ce kan lamarin da zarar mun same shi.

Wannan layi ne

Wasu labaran da za ku so ka kalla

Wannan layi ne

Ana iya cewa a yanzu Sheikh Abduljabbar yana jiran ganin yadda al'amura biyu za su kaya masa, ɗaya matakin da gwamnati za ta ɗauka sakamakon muhawarar, sai kuma yadda za ta kaya tsakanin sa da Sheikh Pakistan.

Masu sharhi na ganin daga cikin fatan Malam Abduljabbar shi ne gwamnati ta buɗe masa masallacinsa da kuma ba shi damar ci gaba da karantarwa, musamman ganin cewa ya nemi afuwa kan zarge-zargen da ake yi masa.

Wannan layi ne