Mohamed Bazoum: Shugaban Nijar ya cika kwana 100 kan karagar mulki

Asalin hoton, EPA
A ranar Litinin din nan Shugaba Mohamed Bazoum na Jamhuriyar Nijar ke cika kwana 100 da hawa kan karagar mulki.
A farkon watan Afrilun 2021 ne Shugaba Bazoum ya sha rantsuwar kama aiki.
Mutane da dama na ganin akwai alamun yiwuwar samun sauyi a fannoni da dama musamman yadda tun farkon mulkinsa, shugaban ya yi alkawarin jajircewa wajen magance matsalar tsaro da kuma kokarin shimfida adalci a mulkinsa.
Wasu kuma na auna mizanin mulkin Bazoum da tsohon shugaban ƙasar, Issoufou Mahamadou.
Kamun ludayinsa
Tuni ƴan siyasa da masu fafutuka suka fara bayyana ra'ayoyi kan yadda suke kallon salon kamun ludayin na Bazoum bayan wadan nan kwanaki.
Alhaji Idi Abdou, wani ɗan fafutukar farar hula a Yamai ya ce akwai abubuwa da dama da shugaba Bazoum ya yi da ya cancanci yabo.
"Kuzarin da ya yi wuya wajen yaki da cin hanci, Bazoum ya kwatanta". in ji Alhaji Idi Abdou.
Ya kuma ce shugaban ya nuna jajircewa wajen kwatanta ƙudirinsa na ganin ana kashe kudin ƙasar ta hanya mai kyau.
Sai dai Alhaji Salisu Amadou na kungiyar farar hula ta RNDD ya ce lokaci bai yi ba na bayyana nasarar Bazoum ko akasin haka.
A ganinsa, magana kadai ba ta wadatar ba, abu mafi mahimmanci shi ne aiwatar da duka alkawuran da ya dauka don tabbatuwarsu - samun zaman lafiya da samun makarantu da asibitoci.
Kakakin Jam'iyyar adawa ta Modern Lumana, Bane Ibrahim ya ce shugaba Bazoum ya kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali tsakanin yan siyasa a ƙasar.
"Mun ga shi ba shi da keta a cikin siyasa, tun da ya zo ya ba mutane da dama su gana da shi a fadar shugaban kasa".
Sai dai a cewarsa, aikin da ya ragewa shugaban shi ne na yaki da cin hanci da rashawa.
Habilu Amadou, kakakin Jam'iyyar adawa ta MPN yana ganin an samu ci gaba a mulkin shugaban sai dai ya bayyana fatan kada salon ya kasance na yaudara.
Amma Alhaji Mai Bukar, ɗaya daga cikin na hannun daman Shugaba Bazoum ya ce yaudara ba ta daga cikin halin Shugaba Bazoum.
"Mutum ne mai adalci, mai tsinkayen nesa kuma mutum ne da ba ya rike komai kankankan". in ji Alhaji Mai Bukar.
Ya kuma ce babu mamaki kan yadda al'ummar kasar suke danganta salon mulkin Mulkin Mahamadou Issoffou da na Shugaba Bazoum saboda kowa da salon mulkinsa.









