Birtukan Mideksa: Tsohuwar fursunar siyasa da ke shugabancin hukumar zaben Ethiopia

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Haimanot Ashenafi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Amharic
- An wallafa
Bayan ta fita daga kangin fursunar siyasa ta tsere kasar Amurka, a yanzu Birtukan Mideksa ta zama wadda ido ya koma kanta a kasar waje a zaben 'yan majalisa na farko tun bayan hawan firaiminista Abiy Ahmed karagar mulki a shekarar 2018, wanda ya sha alwashin kawo karshen mulkin mulaka'u na shekaru da dama.
Yayin da yake bayyana sunan Ms Birtukan, mai shekara 47, a matsayin jagorar hukuma mai matukar muhimmanci wato hukumar zabe, sabon Firimiyan ya bayyana ta a matsayin wadda ba za ta taba mika wuya ba ko da kuwa ga gwamnati ne.
Yawancin mutanen da ke wurin sun amince da bayanansa, saboda ta shahara wajen jarumta da jajircewa a matsayinta na lauya, kuma alkali sannan 'yar siyasa.
A shekarar 2001 Mis Birtukan ta tsaya takarar 'yar majalisa amma ba karkashin kowacce jam'iyya ba, sai dai sai ta sha kaye a hannun jam'iyyar hadaka ta Ethiopian People's Revolutionary Democratic Front (EPRDF), sannan ta amince cewa shan kayen nata ya samo asali ne saboda ba ta yi suna ba, ba wai aringizon kuri'u aka yi ba.
Daga nan sai ta zama Alkali, shekara guda bayan nan ta kuma dauki hankalin jama'a a lokacin da ta yi wani namijin kokari ta hana 'yan siyasa tsoma baki a fannin shari'a tare da bayar da umarnin a saki tsohon ministan tsaron Habasha Siye Abraha daga kurkuku.
Ana ganin kamen da aka yi masa kan zargin cin hanci da rashawa ya na da nasaba da kalubalantar firaiministan wancan lokacin Meles Zenawi.
Wani abokinta da bai so a bayyana sunan shi ba ya ce "Batun Siyes abu ne da aka sani a bayyane. Amma ita Mis Birtukan da sauran alkalai sun dade suna kokarin kalubalantar tsarin da ake bi.''

Asalin hoton, AFP
Saboda gagara samun kwanciyar hankali, Mis Birtukan ta sake komawa fagen siyasa, inda ta taka muhimmiyar rawa wajen hadakar jam'iyyar Coalition for Unity and Democracy (CUD) domin yakar jam'iyyar EPRDF a zaben 'yan majalisu na shekarar 2005, wanda aka yi wa kallon mafi zafi a tarihin siyasar kasar Habasha, wanda 'yan adawa suka yi ikirarin an yi musu kwace.
A matsayinta na babbar jami'ar hadakar jam'iyyun CUD, Mis Birtukan ta kasance wadda jami'an tsaro ke farauta, tana cikin dubban mutanen da aka tsare bayan zaben da aka gudanar. Kuma kusan mutane 200 'yan sanda suka kashe a wancan lokacin.
Yanke hukunci
An rushe ginin da jam'iyyar CUD, to amma daga gidan kurkuku shugabannin jam'iyyar ciki har da Mis Birtukan suka sake gina shi tare da sauya mata suna zuwa Kinjit International Council (KIC), wadda manufarta shi ne karfafa dimukradiyya.
"Lokuta da dama suna tattaunawa da kuma daukar mataki ne a kan hanyar su ta zuwa kotu,'' in ji wani makusancin Mis Birtukan.

Asalin hoton, AFP
A shekarar 2006, Mis Birtukan na daga cikin daruruwan mutanen da aka tsare, ciki har da shugaban hukumar kare hakkin dan adam na Habasha Daniel Bekele - inda ake zargin su da laifuka daban-daban ciki har da cin amanar kasa.
Abin da ya kada su shi ne daya daga cikin masu gabatar da karar sananne ne wato Shimels Kemalne kuma abokin Mis Birtukan, sannan gida daya suke da Mista Daniel - wanda ya bukaci alkali ya yanke musu hukuncin kisa.
"Yanayin wurin ya zama abin mamaki," in ji abokin aikinta, wanda ya san su a lokacin da ya yi hira da sashen Amharic na BBC.
"Sam Shimels bai sassauta ba, ya hada siyasa da wani abu na kashin kansa. Yana ganin abokansa sun ci amanarsa saboda sauya akida.''
Sai dai alkalin ya yi watsi da bukatar mai shigar da karar, maimakon haka ya yanke musu hukuncin daurin rai da rai.
An tilasta wa Mis Birtuka barin 'yar karamar 'yarta a hannun mahaifiyarta da tsufa ya riske ta, a haka ta fara zaman kason da aka yanke ma ta a gidan kurkukun Kaliti mai matukar hadari, inda ta zama jagorar wanzar da zaman lafiya tsakanin 'yan aware na jam'iyyar CUD da suka balle, bayan samun sabani da rarrabuwar kawuna.
"Ba ta magance matsalar ba, amma sun gina wata sabuwar kungiya ta karkashin kasa, kuma sun yi nasara," in ji abokinta.
A gidan kaso, tana daga cikin fursunonin da suka shiga tattaunawa da kungiyar dattaijai da suka yi kokarin sasanta su da bangaren gwamnati.
Wannan ya sanya an sake ta a shekarar 2007, bayan shafe watanni 18 a kaso, inda ta sanya hannu kan wasu takardun nuna nadama ga abin da suka aikata bisa kuskure, Mis Birkuna na daga cikin wadanda suka nemi afuwar firaiminista Meles.
Matakin ya janyo ce-ce-ku-ce daga bangaren 'yan adawa, ta kuma yi kokarin ganin ba ta yi amfani da batun ba a wani jawabi da ta gabatar a kasar waje.
A wancan lokacin shugaban 'yan sanda Wokneh Gebeyehu - yanzu kuma sakataren tsaro ya ba ta umarnin ta nemi afuwa tare da zarginta da ketare dokokin da aka shinfida mata kafin a yi mata afuwa.
To amma Mis Birtukan ta ki yin hakan, a kuma lokacin bikin Kirsimatin shekarar 2008, aka sake mayar da ita gidan kaso domin ta kammala daurin rai da rai da aka yanke mata tun da fari.

Asalin hoton, AFP
A wata makala da aka wallafa a jaridar Negar ta kasar, jim kadan bayan sake kama ta, ta rubuta cewa: "Watakila wannan ne kalamina na karshe," sannan gabannin ce-ce-ku-cen da aka dinga yi kan matakin da ta dauka na neman afuwa ta rubuta cewa: "Na rattaba hannu kan takardun nan. Wannan shi ne abun da ba zan iya sauyawa ba, ko da na so yin hakan."
Ta kara shiga tsaka mai wuya lokacin da aka sake mai da ta gidan kaso, an killaceta awani wuri mai wuya na watanni biyu, an kuma haramta ma ta ganin 'Yarta.
Guduwa Amurka
Wannan ya kara janyo ma ta tausayi daga al'umma, kungiyar kare hakkin dan adam tata kira ta da sunan fursunar cimma buri, yayin da jaridun Afurka ta Kudu wato Mail da Guardian suka bayyana ta da fitacciyar fursunar siyasa ta kasar Habasha.
A watan Oktoba 2010 Mis Birtukan ta sake samun 'yanci, bayan sasantawa kan wata afuwa.

Asalin hoton, AFP
Bayan an sake ita, sai ta dauki 'yarta suka tsere Amurka, inda ta yi karatu a jami'ar Harvard Kennedy, daga bisani ta yi aiki a hukumar tabbatar da dimukradiyya ta Amurka wadda ke taimakawa mulkin dimnukradiyya a fadin duniya.
Ta sake komawa gida bayan Mista Abiy ya zama firai minista. Sai dai nadin ta a wannan mukami na cike da sarkakiya, bayan shafe lokaci mai tsaho ana tsaiko a ranar Litinin 21 ga watan Yuni 2021 za a gudanar da zabe a kasar Habasha, duk da cewa yawancin jam'iyyun adawa sun kauracewa zaben saboda zargin ba za a yi adalci ba.

Asalin hoton, AFP
Cikin masu kalubalantar Mis Birtukan akwai farfaesa Merera Gudina, wanda ya santa shekaru 21 da suka gabata. Shi ne shugaban jam'iyyar Oromo Federalist Congress (OFC), wadda ta sanar karara ba za ta shiga zaben ba.
"Ba mu ga alamun cibiyoyin zabe na gaskya ba, ba kuma mu ga alamun za a samu 'yan takara na kjwarai ba domin haka ba za mu shiga zaben ba ," in ji shi.
Ya kara da cewa: ''Wata jam'iyyar daga yankin Omromia ma ta sanar da kauracewa zaben, idan aka hada da tashin hankalin da ake yi a yankin Tigray, za a lura kusan yankin Amhara ne kadai za su gudanar da wannan zabe sai kuma babban birnin kasar Addis Ababa.''
Ita kan ta Mis Birtukan za ta rage abubuwan da take fata na zaben. A wata wasika da ta aikewa majalisar Amurka a watan Mayu, ta yi gargadin cewa "Ba za a iya kaucewa kura-kurai ba, musamman a dimukradiyya, yayin da al'adun siyasar ke matukar sauyawa, da kuma rashin tsaro."










