Ganges river: Matuƙin jirgin da ya ceci jaririya a cikin kogi ya sha yabo a Indiya

The baby girl found in the wooden box

Asalin hoton, Anil Kumar

Bayanan hoto, An kai jaririyar mai kwana 21 asibiti
An wallafa

Wani matuƙin kwale-kwale a jihar Uttar Pradesh da ke arewacin Indiya ya sha yabo bayan da ceci wata jaririya da ya same ta a cikin akwatin katako a cikin kogin Ganges.

Gullu Chaudhary ya ce kukan jaririyar mai kwana 21 ne ya ja hankalinsa, wacce aka lulluɓe ta a cikin jan majanyi aka sanya ta a akwatin katako da aka yi wa kwalliya da ababen bautar addinin Hindu.

An kai jaririyar asibiti kuma ana kula da lafiyarta. Daga baya za a kai ta gidan kula da marayu.

Jami'ai na bincike kan yadda aka samu jaririyar a cikin kogi.

Ba su dai fara tunanin yiwuwar cewa jefar da ita aka yi ba, sai dai Indiya na daga cikin ƙasashen da suka fi fama da wariyar jinsi mafi muni a duniya.

Ana yawan nuna wa mata wariya sannan ana ganin haihuwar ƴaƴa mata a matsayin wahala, musamman a tsakanin al'ummomi marasa ƙarfi.

Duk da cewa a kan zubar da cikin yara mata da taimakon ƙananan asibitocin da ke zubar da ciki ba bisa ƙa'ida ba, ba a faye samun matsalolin kashe jarirai ko jefar da su ba bayan an haife su.

The baby girl in the wooden box

Asalin hoton, Anil Kumar

Bayanan hoto, An lulluɓe jaririyar cikin jan majanyi aka sanya ta a akwatin katako da aka yi wa kwalliya da ababen bautar addinin Hindu

Ƴan sanda sun ce a jikin akwatin an maƙala wata takarda da ke ɗauke da rana da lokacin da aka haifi jaririyar, sannan an rubuta cewa sunanta Ganga - da ke nufin kogin Ganges a ƙabilar Hindu.

Gwamnatin jihar ta ce za ta ɗauki ɗawainiyar kula da jaririyar. Babban Minista Yogi Adityanath ya sanar da cewa gwamnati za ta bai wa matuƙin kwale-kwalen tukuwici, da ya haɗa da gida kan nuna halayyar "jin ƙan ɗan adam marar misali."

Jami'ai a gundumar Ghazipur inda aka ceci jaririyar, ya shaida wa manema labarai cewa Majistaren Gundumar, MP Singh ya je ya duba jaririyar sannan an tura jami'ai don su gana da matuƙin jirgin.

Mr Chaudhary ya ce a yayin da mutanen da suke bakin kogin suka ji kukan jaririya babu wanda ya damu da ya taimaka. "Amma sai na yi maza na je na cece ta. Da na buɗe akwatin katakon sai na ganta a ciki."

Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin mutanen da suka taru a bakin kogin. Bidiyon da aka ɗauka a wajen sun nuna yadda matuƙin jirgin yake ɗaukar akwatin daga cikin ruwan yana ɗauke da ita yana jijjiga ta a hannunsa.

Daga nan sai ya tafi da jaririyar gidansa inda ƴan sanda suka ɗauke ta sannan jami'an cibiyar kula da walwalar mutane suka kai ta asibiti.