Ramadan: Hotunan makon farko na watan Azumi

An wallafa

Miliyoyin musulmi na gudanar da azumin watan Ramadan, wata guda na azumi da gudanar da addu'o'i.

Musulmai na gudanar da ibada a masallaci

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Musulmi sun yi sallar Tarawih ta farko a cibiyar Diyanet da ke birnin Washington, a Amurka, ranar 13 ga watan Afirilu

Wannan shi ne azumin watan Ramadan na biyu da aka yi shi cikin annobar korona, hakan na nufin wasu al'umomin za su yi azumi cikin taka-tsantsan da bin ka'idojin kariya daga cutar.

Masu azumi ba za su ci abinci ko shan ruwa ba a tsawon yini guda, har sai zuwa faduwar rana.

Azumi ibada ce mai matukar muhimmanci, wadda ke kusanta bawa da ubangijinsa, da kara lafiya da kuma koyarwa ta fannoni da dama.

Ga wasu daga cikin hotuna daga sassa daban-daban na duniya, kan yadda wasu musulmi suke gudanar da ibada a watan azumin Ramadan.

Musulmai na duba wata ta amfani da abin hngen nesa lokacin da rana ta fadi

Asalin hoton, Shutterstock

Bayanan hoto, Musulmai na duba watan Ramadan ta amfani da abin hangen nesa, a ranar 12 ga watan Afirilu a yankin Palembang, na Indonesia

Ana yin azumin Ramadan a watan 9 na addinin Musulunci, inda ake farawa da ganin watan wanda aka fi sani da hilal.

Katuwar fitilar kwai mai launi daban-daban.

Asalin hoton, Shutterstock

Bayanan hoto, Ranar 12 ga watan Afirilu, ma'aikata a Zirin Gaza sun sanya katuwar fitilar kwai ta gargajiya, wadda ita ce alamar watan Ramadan da aka fara yin hakan shekaru 800 da suka wuce.

Watan Ramadan lokacin ibada ne mai matukar muhimmanci ga al'ummar musulmi.

Sannan daya daga cikin shika-shikan musulunci guda biyar, wanda ya zama wajibi ga kowanne musulmi ya aikata su, kamar yadda Allah SWT ya umarta.

Haka kuma kauracewa ci da sha a tsahon yin, Ramadan lokaci ne da ake son musulmai su yawaita sadaka, da kara kusanci da Ubangiji , da nuna karamci da kyautatawa.

Ma'aikata akan tsani su na makala fitilar kwai

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar 12 ga watan Afirilu, a birnin Najaf na Iraqi, ma'aikata na sanya fitilar kwai da ake ado da ita a lokacin azumin watan Ramadan.
Mutane a tsaye a gabar teku lokacin da rana ke shirin faduwa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Al'ummar Indonesia sun yi ninkaya, a wani bangare na bikin gargajiya da ake kira Padusan domin taron watan Ramadan a tekun Parangtritis da ke Yogyakarta, ranar 12 ga watan Afirilu 2021. Padusan na nufin ninkayar wanke zunubi kamar yadda, gabanin fara Azumi.

Yayin da aka fara azumin Ramadan a ranar 12 ga watan Afrilu, yawancin musulmai za su sha wuya wajen amfani da dokokin kariya daga cutar korona, da za su hana su yin wasu bukukuwan al'ada.

Ma'aikata na feshin magani a masallaci

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ma'aikata na feshin magani a masallaci, domin rage yaduwar cutar korona a ranar farko da fara azumin Ramadan a Peshawar a Pakistan

Yawanci a Birtaniya iyalai suna zaman yin buda-baki ne tare da 'yan uwa da abokan arziki, amma saboda dokar kulle, haduwar za ta yi wuya.

Har wa yau, duk da cewa an haramta taruwar mutane da yawa a lokacin Azumin Ramadan na bara, wannan shekarar watan ya zo ne daidai lokacin da aka fara sassaut dokar kulle a wasu yankunan kasar.

An amince sama da mutum shida su hadu a waje, sannan gidajen sayar da abinci za su dinga sayar wa mutane abinci a waje.

Amma a wasu yankunan na duniya an sanya dokokin da suka hada da sanya takunkumi a lokacin ibada da sauran wurare.

Masallaci an yi masa ado da fitilun da suka rubuta Ramazan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hoton cibiyar Diyanet da ke birnin Washington a Amurka
Musulmi na sallah sanye da takunkumin rufe fuska

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Musulmai sun yi sallar Tarawih ta farkon watan azumin Ramadan a cibiyar Diyanet da ke birnin Washington a Amurka
Musulmai na gudanar da salla a masallaci

Asalin hoton, Getty Images

Musulmai na yin salla a masallaci

Asalin hoton, Anadolu Agency

A wani sako da hukumomin Hadaddiyar Daular Larabawa ta wallafa a shafin Twitter, an bukaci mutane su kiyaye taruwa a lokacin azumi, su takaita ziyarar 'yan uwa, da kiyaye rarraba abinci tsakanin gidaje da iyalai.

Matasa biyu na karatun Alkur'ani

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Matasa biyu na karatun Alkur'ani lokacin azumi a masallacin Banda Aceh, a Indonesia
Dalibai sun yi sahu su na salla

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Dalibai musulmai na yin sallah a cikin ajinsu a makarantar kwana ta Sirajussa'adah da ke Depok, a yammacin Java, da ke Indonesia

A Bangladesh, gwamnati ta sanar da tsauraran matakan kulle na mako guda, daga 14 ga watan Afirilu.

Hoton yadda kasuwar kayan lambu ta Barishal, ke ci a Bangladesh

Asalin hoton, Shutterstock

Bayanan hoto, Mutane sun fito kasuwar said kayan lambu da ke garin Barishal a Bangladeshi, ranar 13 ga watan Afirilu gabannin shiga dokar kulle
Mutane na jin dadin shagalin zagayowar waran Ramadan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mutane na jin dadin shagalin fara azumi a tsohon birnin Mosul na kasar Iraqi, ranar 13 ga watan Afirilu
Yara na rawa su na kewaya fitilar kwai a tsohon garin Mosul na Iraqi

Asalin hoton, Getty Images

Yara sun tsaya an dauke su hoto sanye d tufafi masu kyau, a bayansu akwai zanen hoton masllacin tsohon masallacin Mosul, a gefe guda kuma akwai tagar tsohon birnin Mosul da ke Iraqi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yara sun tsaya an dauke su hoto sanye da tufafi masu kyau, a bayansu akwai zanen hoton tsohon masallacin Mosul
Matashi na karatun alkur'ani a gida

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani mutum yana karatun Alkur'ani a birnin Panama, gabanin shan ruwa a ranar farko da fara azumin watan Ramadan
Wani mai ibada ya na zaune a gida ya na karanta Alkur'ani

Asalin hoton, AFP

Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka.