Ramadan: Hotunan makon farko na watan Azumi

An wallafa

Miliyoyin musulmi na gudanar da azumin watan Ramadan, wata guda na azumi da gudanar da addu'o'i.

Wannan shi ne azumin watan Ramadan na biyu da aka yi shi cikin annobar korona, hakan na nufin wasu al'umomin za su yi azumi cikin taka-tsantsan da bin ka'idojin kariya daga cutar.

Masu azumi ba za su ci abinci ko shan ruwa ba a tsawon yini guda, har sai zuwa faduwar rana.

Azumi ibada ce mai matukar muhimmanci, wadda ke kusanta bawa da ubangijinsa, da kara lafiya da kuma koyarwa ta fannoni da dama.

Ga wasu daga cikin hotuna daga sassa daban-daban na duniya, kan yadda wasu musulmi suke gudanar da ibada a watan azumin Ramadan.

Ana yin azumin Ramadan a watan 9 na addinin Musulunci, inda ake farawa da ganin watan wanda aka fi sani da hilal.

Watan Ramadan lokacin ibada ne mai matukar muhimmanci ga al'ummar musulmi.

Sannan daya daga cikin shika-shikan musulunci guda biyar, wanda ya zama wajibi ga kowanne musulmi ya aikata su, kamar yadda Allah SWT ya umarta.

Haka kuma kauracewa ci da sha a tsahon yin, Ramadan lokaci ne da ake son musulmai su yawaita sadaka, da kara kusanci da Ubangiji , da nuna karamci da kyautatawa.

Yayin da aka fara azumin Ramadan a ranar 12 ga watan Afrilu, yawancin musulmai za su sha wuya wajen amfani da dokokin kariya daga cutar korona, da za su hana su yin wasu bukukuwan al'ada.

Yawanci a Birtaniya iyalai suna zaman yin buda-baki ne tare da 'yan uwa da abokan arziki, amma saboda dokar kulle, haduwar za ta yi wuya.

Har wa yau, duk da cewa an haramta taruwar mutane da yawa a lokacin Azumin Ramadan na bara, wannan shekarar watan ya zo ne daidai lokacin da aka fara sassaut dokar kulle a wasu yankunan kasar.

An amince sama da mutum shida su hadu a waje, sannan gidajen sayar da abinci za su dinga sayar wa mutane abinci a waje.

Amma a wasu yankunan na duniya an sanya dokokin da suka hada da sanya takunkumi a lokacin ibada da sauran wurare.

A wani sako da hukumomin Hadaddiyar Daular Larabawa ta wallafa a shafin Twitter, an bukaci mutane su kiyaye taruwa a lokacin azumi, su takaita ziyarar 'yan uwa, da kiyaye rarraba abinci tsakanin gidaje da iyalai.

A Bangladesh, gwamnati ta sanar da tsauraran matakan kulle na mako guda, daga 14 ga watan Afirilu.

Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka.