Okonjo-Iweala: Biden ya kawo ƙarshen taƙaddamar da ta hana mace ta farko jagorancin WTO

Gwamnatin Joe Biden ta Amurka ta kawo ƙarshen takaddamar da ta hana naɗa mace ta farko da za ta jagoranci Kungiyar Cinikayya ta Duniya (WTO) bayan da ta bayyana goyon bayanta ga tsohuwar ministar kuɗin Najeriya.
Ngozi Okonjo-Iweala ce ke kan gaba wajen zama mace ta farko da za ta jagoranci ƙungiyar cinikayyar ta duniya kafin gwamnatin Mista Trump ta ce tana goyon bayan wata matar ta daban, Yoo Myung-hee ta Koriya ta Kudu.
A halin da ake ciki, Ms Yoo ta janye daga takarar shugabancin ƙungiyar.
Idan aka tabbatar ma ta muƙamain, Dr Okonjo-Iweala za ta kasance mace ta farko, kuma ƴar Afirka ta farko da za ta jagoranci ƙungiyar.
A watan Oktobar bara kwamitin zabe na ƙungiyar ta WTO ya bayyana sunan Okonjo-Iweala ga mambobin ƙungiyar 164, yana cewa ta dace su zabe ta ta aye gurbin Roberto Azevedo, inji kakakin kungiyar.
Ya ce" "Ƙasa daya ce kawai ta ki goyon bayan Okonja-Iweala".
Ms Okonjo-Iweala, mai shekara 66, ita ce mace ta farko da ta zama ministar kudi da harkokin wajen Najeriya.





