Indiya: An kama wani Musulmi kan yunƙurin 'Musuluntar da budurwarsa ƴar addinin Hindu'

Protesters against the "love jihad" law

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana ta shan suka game da fushin da wannan dokar da ta ɓatawa mutane rai
An wallafa

'Yan sanda a jihar Uttar Pradesh sun kama wani mutum da ake zargi da ƙoƙarin Musuluntar da wata mata 'yrn addinin Hindu.

Shi ne mutumin farko da aka kama ƙarƙashin wannan doka da ke shirin kama masu "soyayya don jihadi" - wani lafazi da masu tsattsauran ra'ayin addinin Hindu ke zargin mazajen Musulmi da su domin auren matansu.

Wannan doka ta janyo ce-ce-ku-ce, abin da masu suka suka kira nuna ƙin jinin Musulunci (Islamophobic).

A ƙalla wasu jihohi huɗu na Indiya sun fara ƙaddamar da wannan ƙudurin doka.

'Yan sanda Uttar Pradesh sun tabbatar da kamun a shafinsu na Twitter a ranar Laraba.

Baban matar ya shaida wa BBC Hindi cewa ya shigar da ƙarar ne saboda matsawa yarinyar da mutumin ya yi tare da yi mata barazana. An yi zargin cewa mutumin yana soyayya da matar ne sai ta yi aure da wani mutum a farkon wannan shekara.

'Yan sanda sun faɗa wa BBC cewa iyalan matar sun shigar da ƙarar ne suna zargin an sace yarinyarsu shekara ɗaya baya, amma an yi watsi da ƙarar ne bayan an gano yarinyar kuma ta musanta zargin.

Bayan an kama shi a ranar Laraba, an aike da shi gidan yari na kwana 14, sai dai ya shaida wa manema labarai cewa bai aikata laifin komai ba kuma "ba shi da alaƙa da matar".

Hukuncin dokar dai shi ne zaman gidan yari na shekara 10, kuma ba a bayar da belin laifin.

Protest against the "love jihad" laws

Asalin hoton, Getty Images

Mecece dokar "soyayya don jihadi"?

A watan Nowamba, jihar Uttar Pradesh ita ce ta farko da ta fara amincewa da ƙudurin doka kan "Tilastawa" ko kuma "Yaudara" da sunan sauya wa mutum addini.

Bai zama dole ta wuce jihohi huɗu ba - Madhya Pradesh da Haryana da Karnataka da kuma Assam - kuma dukansu suna buƙatar gabatar da doka kan "soyayya don jihadi".

Duka waɗannan jihohi biyar jam'iyyar BJP mai mulki ce ke jagorantarsu, waɗanda ake zargi da kafa dokar ƙin Musulmai.

Masu suka sun kira wannan doka ta cin zarafi, wasu na nuna damuwa kan cewa dokar za ta iya janyo ana cin zarafin mutane, yadda mutane ke amfani da soyayyar jihadi a matsayin wani ikirarin laifi, wanda a hukumance ba a yarda da shi ba.

Masu sukar jam'iyyar BJP sun ce matsalar addini na ƙaruwa tun lokacin da Firaminista Narendra Modi ya karɓi mulki a 2014.

Tun a baya dama a kan tantance auren Musulmai da 'yan addinin Hindu amma wanda ake yi a bayan nan ya ɗauki wani salo na daban.