EFFC za ta binciki Ma'aikatar Ayyuka da Gidaje da Makamashi kan badaƙalar N4.5bn

An wallafa

Hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC, ta ce za ta fara gudanar da bincike kan badaƙalar wasu miliyoyin nairori a Ma'aikatar Ayyuka da Gidaje da Makamashi ta ƙasar kafin daga bisani a raba ta gida biyu.

Hukumar ta ce ta ɗauki wannan alwashin ne sakamkon rahoton da wata jarida ta bankaɗo kan yadda a cikin watanni hudu aka biya waɗannan makudan kudade cikin asusun ajiyar wasu ma'aikata 21 na tsohuwar ma'aikatar.

Duk da cewa bai amince a naɗi muryarsa ba, kakakin hukukar ta EFCC Wilson Uwujaren ya tabbatar wa BBC cewa tabbas hukumar ta ɗaura babbar ɗamarar ganin cewa ta gudanar da wannan bincike kan yadda har a cikin watanni hudu kacal, aka biya zunzurutun kuɗaɗen da suka kai fiye da naira biliyan huɗu da rabi a cikin asusun wasu ma'aikata 12 na tsohuwar ma'aikatar.

Malam Ado Adamu Also jami'in hulɗa da jama'a na Ministan Wutar Lantarki na Najeriyar, kuma ya shaida wa BBC cewa sun samu takarda daga hukumar EFCC game da batun badaƙalar kuɗaɗen, kuma za su yi bincike ne kan abubuwan da suka faru daga shekara ta 2015 zuwa 2019 a tsohuwar ma'aikatar.

Ya ce: ''An rubuto mana an nuna mana cewa akwai jami'an da ake zarginsu da waɗannan abubuwa. Mu kuma mun buɗe musu hanya, Minista ya ce mu ba su goyon baya su yi duk binciken da suke buƙata.

''Sai dai waɗanda ake zargin aka aiko wa takardar ba ma'aikatar ba. Masu bincike sun nemi bayanai, sannan mutanen na ba da bayanan kan abin da suka sani.

''Amma Minista ya ce dole duk wanda ake zargi ya ba da kansa a yi duk binciken da ya kamata,'' a cewar Adamu Also.

A nata ɓangaren, jam'iyyar adawa a kasar PDP, ta fitar da wata sanarwa inda take ƙalubalantar Ministan Ma'aikatar Ayyuka da Gidaje Babatunde Fashola da ya yi gaggawar fitowa ya wanke kansa game da wannan rahoto da ya bankaɗo badakalar kudaden.

Sannan ta kuma ƙalubalanci gwamnatin Najeriya da ta fiito ta yi bayani wa ƴan kasa game da batun, wanda ta ce ya shafi kashe kuɗaɗen jama'a idan dai da gaske take yi game da yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasar.

Kawo yanzu dai hukumar ta EFCC ba ta bayar da taƙamaimen lokacin da za ta fara gudanar da wannan binciken gadan-gadan ba, ko da yake ta yi alwashin cewa abu ne da ba za ta yi sanyin gwiwa a kai ba.