Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chadi: Shirin Najeriya na ba Chadi wutar lantarki ya janyo ce-ce-ku-ce
Wasu 'yan Najeriya kansu ya ɗaure game da samar wa ƙasar Chadi wutar lantarki da gwamnatin ƙasar ke shirin yi.
Tun a ranar Alhamis 22 ga watan Oktoba Ministan Wutar Lantarki na Najeriya Sale Mamman ya bayyana cewa Ministar Makamashi ta Chadi, Ramatou Mahamat Houtouin ta kawo masa ziyara.
Daga cikin abin da suka tattauna akwai yiwuwar Najeriya ta fara samar wa da ƙasarta wutar lantarki.
"Sashen lantarki na Najeriya na da damar zama wata kafar samar da kuɗaɗen ƙasar waje [ga ƙasar], yayin da muke ƙoƙarin faɗaɗa harkokin tattalin arziki," in ji ministan.
Ministan ya ƙara da cewa "Abin da muka tattauna kenan da ministar [Ramatou Mahamat Houtouin]; yiwuwar samar wa Chadi wutar lantarki daga Najeriya."
"Yayin da muke ƙara ƙoƙari wurin kyauta samar da wutar a gida, muna kuma son mayar da Najeriya wata madogarar wurin samar da lantarki a yankin Afirka ta Yamma."
Sai a ranar Lahadi ne kuma kamfanin rarraba lantarki na Najeriya Transmission Company of Nigeria (TCN), mallakar gwamnati, ya sanar da aniyar gwamnatin.
TCN ya ce gwamnatin Chadi ta miƙa wa Najeriya buƙatarta ta neman a saka ta cikin tsarin samun lantarki daga Najeriya - abin da ya jawo martani iri-iri daga 'yan ƙasar.
Me ƴan Najeriya ke cewa?
Tsohon sanata mai wakiltar mazaɓar Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce wannan tunani na gwamnatin tarayya babu kan-gado.
"Tunanin Gwamnatin Tarayya na kai lantarki zuwa Chadi yayin da muke cikin duhu shirme ne," in ji tsohon sanatan.
Ita ma 'yar gwagwarmaya Aisha Yesufu ta yi martani, tana mai cewa "Wayyo Allahna, Najeriya ba ta taɓa samar da lantarki ta awa 12 a duka jiha 36 ba amma yanzu tana neman bai wa Chadi wutar."
Al'ameen (@Al_ameen_Yabo) cewa ya yi: "Najeriya na samar da lantarki ga Togo da Niger da Benin, yanzu kuma tana son fara bai wa Chadi yayin da muke fafutikar samun ta 12 a kullum."
Ƙarfin samar da lantarki a Najeriya
Samarwa da rarraba wutar lantarki abu ne da ya jima yana jawo ce-ce-ku-ce duk lokacin da aka yi maganar makamashi.
Adadin yawan wutar lantarki a Najeriya yana reto tsakanin ma'aunin megawatts 3,000 zuwa 4,500 a 'yan shekarun nan.
A yanzu haka Najeriya na samar wa ƙasashe maƙwabta guda uku da wutar lantarki; Jamhuriyar Nijar da Benin da Togo.
Bayanai daga shafin Nigerian Electricity System Operator sun nuna cewa, an samar da jumillar lantarki megawatts 3,474.5MW ya zuwa ƙarfe 6:00 na safiyar Lahadi, wanda raguwa ce daga 3,776.5MW da aka samar ranar Asabar.