Sale Mamman: Ministan lantarki na Najeriya ya ce an samu sauyi zamanin Buhari

    • Marubuci, Haruna Kakangi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-media Broadcast Journalist
  • An wallafa

Ministan Wutar Lantarki a Najeriya Injiniya. Saleh Mamman ya ce an samu ci gaba sosai kan yadda ake samun wutar lantarki a fadin kasar.

Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawar musamman da aka yi da shi a shirin A Fada A Cika na BBC da hadin gwiwar Gidauniyar MacArthur.

Ministan ya kalubalanci duk wanda yake da ja dangane da ikirarin nasa.

Amma ministan ya ce yanzu haka gwamnati na yunkurin ganin ta magance karancin wutar lantarki a kasar bayan gano matsalolin da ke addabar bangaren.

A cewarsa matsalar wutar lantarki al'amari ne babba, wanda ke bukatar makudan kudade da lokaci kafin a magance.

Najeriya ta dade tana fuskantar karancin wutar lantarki, wani abu da ake kallon shi ne sila na durkushewar masana'antu da dama.

Masana sun ce matsalar na hana masu zuba jari shigowa kasar domin kafa kamfanoni.

Gwamnatoci da dama sun sha yi alkawurran cewa za su kawar da matsalar karancin wutar lantarki, sai dai har yanzu babu wata gwamnatin da ta iya yin hakan.

A lokacin da ya kama mulki, shugaban kasar na yanzu Muhammadu Buhari ya ce "Babu wani abu da ke matukar yin zagon kasa ga tattalin arzikin Najeriya kamar rashin wutar lantarki a tsawon shekarun nan.Ba za mu bar wannan al'amari ya ci gaba ba."

Ana nan ana yin nazari domin gano hanya mafi sauri kuma mai inganci ta samar da lantarki cikin sauki ga al'ummar Najeriya."

Sai dai ko bayan shekara biyar da hawansa kan karagar mulki, al'umma da dama na ganin cewa ba a samu wani ci gaba na a-zo-a-gani ba game da wutar lantarkin.

Wata mai sana'ar sayar da kifi da kaji da ke a garin Madalla mai suna Fatima Nurudeen ta ce "Mukan yi asara, sau da dama mukan zubar da kajinmu, da kifi saboda rashin wutar lantarki."

Haka nan ma wani mai suna Mashkur Muhammad daga jihar Kano ya ce "Za ka ga ba a bayar da wutar yadda ya kamata, idan an kawo (Wutar lantarki) ba za ta wuce awa daya ko biyu ba an dauke."

Shi kuma Muhammad Musa ya ce "A baya sukan kawo mana bil(Takardar biyan kudin wuta) ne na gidan baki daya amma yanzu daki-daki ake kawo bil, kuma ga shi ba mu samun wutar sosai."

Sai dai a tattaunawar da ya yi da BBC ta awa daya a cikin shirin A FADA A CIKA, ministan wutar lantarki na Najeriya Saleh Mamman ya ce gwamnatin shugaban kasar Muhammadu Buhari ta karbi mulkin kasar nan a lokacin da karfin wautar lantarki da ake samu bai wuce megawatt 3000 ba, amma bayan kama mulkin shugaban akwai lokacin da aka iya samar da karfin wutar lantarki megawatt 5000.

Ya kuma ce al'ummar kasar sun shaida haka "Kashi 80 zuwa 90 cikin dari na 'yan Najeriya masu samun wutar lantarki sun san cewa an samu canji."

Sai dai ministan bai tabbatar da sahihancin wannan kididdiga tasa ba.

'Manyan matsalolin da muka gano'

Ministan na wutar lantarki ya zayyano wasu daga cikin matsalolin da ya ce su ne suka sanya aka kasa magance matsalar wutar lantarki a kasar...

  • Cin hanci
  • Rashin yin aiki tsakani da Allah
  • Rashin daidaito tsakanin hanyoyin rarraba wutar lantarki da karfin wutar lantarki da ake samarwa

Sai dai a cewarsa suna daukan matakan kawo karshen wadannan matsaloli.

Ina aka kwana kan aikin cibiyar samar da wutar lantarki ta Mambila?

Aikin cibiyar samar da wutar lantarki ta Mambila al'amari ne da ya kwashe sama da shekara 40 ana magana a kansa - a cewar ministan.

A lokacin tattaunawar, wani dan jarida Simon Sunday ya tambayi ministan shin ina aka kwana game da aikin samar da wutar lantarki na Mambila?

Minista Saleh Mamman ya ce yanzu haka ana kan aikin safiyo na wurin da za a samar da cibiyar bayan cimma yarjejeniyar samun filin da gwamnatin jihar Taraba.

A cewar sa "Fadin wannan wuri ya kai murabba'in kilomita 3,500".

Inda ya ce ana yin aikin safiyon ne ta sama da ta kasa "Yanzu masu safiyo ta sama sun kammala, saura masu yi ta kasa, ruwan sama da matsalar cutar korona ne suka hana a kammala."

Ya ce gwamnatin na kokarin ganin ta fara wannan aiki, inda za a karbo bashin kudaden da za a yi aikin daga banki.

Yarjejeniya da bunkasa samar da wutar lantarki

A shekarar 2019 ne kasar ta Najeriya ta sanya hannu da wani kamfanin kasar Jamus domin bunkasa samar da wutar lantarki.

Ministan ya ce aikin da kamfanin zai yi shi ne ya daidaita ingancin kayan rarraba wutar lantarki da wutar lantarki da ake samarwa daga cibiyoyin samr da wutar.

A cewar sa cutar korona ce ta hana a fara gudanar da aikin.

Latsa nan domin kallon cikakken shirin.

Shirin A FADA A CIKA na zuwa ne tare da tallafin gidauniyar MacArthur