Buhari ya sake naɗa Farfesa Mahmood Yakubu shugaban INEC

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake gabatar da sunan Farfesa Mahmood Yakubu, a majalisa domin sake ci gaba da jagorantar hukumar zabe a wa'adi na biyu.
Shugaba Buhari ya tabbatar da sake naɗa Farfesa Yakubu ne a cikin wata wasika da ya aika wa shugaban majalisar dattiajai Sanata Ahmed Lawan, kamar yadda mai magana da yawunsa Femi Adesina ya bayyana a cikin wata sanarwa.
Shugaban ya ce "bisa tanadin sashi na 154 (1) na kundin tsarin mulki na 1999 (Wanda aka yi wa kwaskwarima). Ina farin cikin gabatar da Farfesa Mahmood Yakubu ga majalisa domin tabbatar da shi a matsayin Shugaban, Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC) a karo na biyu kuma wa'adi na ƙarshe. "
Kafin tabbatar da sake naɗinsa sai majalisa ta amince.
A watan Oktoba 2015 ne Shugaba Buhari ya naɗa Farfesa Yakubu a matsayin shugaban hukumar INEC, wanda ya maye gurbin Farfesa Attahiru Jega.
Farfesa Yakubu shi ya jagoranci babban zaben shekarar 2019, da kuma na gwamnoni da ake gudanarwa lokaci daban da babban zaɓe.
Kuma duk da cewa yawancin zabukan da ya jagoranta sun sha suka daga masu sa ido na cikin gida da na kasashen waje kan matsaloli da zargin magudi, amma kuma an yaba masa a zaben gwamnoni da ya jagoranta a baya-baya nan a jihohin Edo inda ɗan takarar jam'iyyar PDP mai hamayya ya lashe da kuma Ondo inda ɗan takarar APC ya yi nasara.





