Italiyawa sun zabi a rage yawan 'yan majalisun ƙasarsu

Italy elections

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Wata ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka yi a Italiya ta nuna ƙarara cewa masu zabe a ƙasar sun goyi bayan rage yawan ƴan majalisar ƙasar da yawansu ya zarce 1,000.

Da alama Italiyawa sun fara gajiya da 'yan siyasar kasarsu, inda jama'a suka zabi a rage yawan 'yan majalisar kasar.

Idan zabin nasu ya kai ga gaci, za a rage yawan 'yan majalisar wakilan kasar Italiyar daga 630 zuwa 400.

Su ma 'yan majalisar dattawan kasar ba su tsira ba, inda za a rage yawansu da kimanin kashi 1 cikin 3.

An dai kafa wannan dokar ne tun bara, bayan da jami'iyyar Five Star Movement - wadda tana cikin hadakar jam'iyyu masu mulkin kasar ta tsaya kai da fata sai an rage girman majalisun kasar.

Ta ce biyan 'yan siyasa kusan 1,000 albashi da alawus-alawus asarar kudaden al'ummar kasar ne.

Ko ya 'yan Italiyan ke kallon wannan yunkurin rage yan majalisun kasar?

Ga abin da wasu 'yan kasar ke cewa:

Alessandro Guiseppe, wanda malamin makaranta ne ba ya zaton za a sami wani gagarumin sauyi:

"Ban san ko wannan matakin zai iya rage kudade masu yawa ba, ganin za a rage 'yan majalisa daga 630 ne zuwa 400 kuma za a rage sanatoci daga 315 zuwa 200. Amma idan abin da 'yan kasar nan ke so ke nan, babu makawa sai mu goyi bayan matakin saboda mulkin dimokradiyya mu ke bi."

Isabella, wata ma'aikaciyar banki kuwa tana goyon bayan matakin ne:

"Rage yawan 'yan majalisun kasa zai taimaka gaya wajen kawo sauki ta bangaren asarar arzikin kasa da ake kashe wa 'yan majalisun da ba sa komai sai dumama kujeru a majalisa maimakon su yi ayyukan da muka aike su - wato wakiltar mu. Amma sai shakara ta 2023 za a fara aiwatar da dokar - wanda shi ne lokacin da ak sa ran wata sabuwar gwamanti za ta karbi ragamar mulkin kasar."

Masana harkokin siyasar kasar ta Italiya na ganin wannan dokar za ta sami karbuwa a fadin kasar. Alkaluman farko da na ra'ayin wadanda suka kada kuri'unsu na cewa fiye da kashi saba'in na 'yan kasar sun goyin bayan daukan matakin.