Yadda likitoci a Yola suka raba tagwaye da aka haifa da hanta ɗaya

Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Yola a jihar Adamawa arewa maso gabashin Najeriya ta yi nasarar raba wasu tagwaye ta hanyar tiyata da aka haifa manne da juna.
Tawagar asibitin da ta kunshi ma'aikata 48 ne ta gudanar da aikin, watanni takwas bayan haifar tagwayen.
Wannan shi ne karo na uku da Asibitin ta FMC Yola ke tiyatar raba tagwaye da aka haifa manne da juna a cewar shugaban cibiyar Farfesa Auwal Abubakar.
Tawagar wacce ta kunshi kwararrun likitocin fida da ma sauran ma'aikatan lafiya ta shafe tsawon sa'o'i uku yayin gudanar da aikin ranar goma ga watan Agusta, da zummar ceto tagwayen biyu mata da aka haifa hanta da hakarkarin su manne da juna.
Jagoran likitocin fiɗar kuma shugaban asibitin FMC Yola Farefesa Auwal Abubakar ya ce an yi tiyatar cikin nasara.
"Hanta ce da haƙarƙari suka zama daya, amma akwai na'urarar da muka yi aiki da ita kuma ta taimaka mana sosai wajen rage zubar jini da kuma kammala aikin cikin ƙanƙanin lokaci," in ji shi.
Farfesan ya ƙara da cewa tun kafun wannan lokacin suka yi niyyar raba 'yan biyun amma sai annobar korona ta tilasta musu yin jinkiri har sai ranar goma ga watan Agusta.
Ya kuma shaidawa BBC cewa yaran na cikin koshin lafiya "sun warke har sun fara wasa bayan kwana uku da gama aikin, "an mayar da su can kauyen su mun yi waya babu wata matsala ko kadan," a cewarsa.

Tagwayen da aka radawa suna Grace da kuma Mercy, mahaifiyarsu Aibekipriye Ebiyenfa ta ce ta sha faɗuwar gaba yayin da aka fara aikin fiɗar saboda rashin tabbas kan makomar 'ya'yan nata.
"A lokacin da suka kira domin yin tiyatar na ɗan tsorata saboda ni 'yar adam ce, sannan a matsayina na mahaifiya na tsorata."
"Ban ji daɗi ba kasancewa ta mace ta farko da ta haifi tagwaye manne da juna ba a garin mu da kuma jaha ta ba."
"Wasu mutanen ma na ta zagina har na fara jin na aikata wani abun kunya, amma yanzu ina farin ciki saboda an yi fiɗar babu wata tangarɗa ga shi yau zamu koma gida" a cewar Mrs. Ebiyenfa.
Matar ta ce tana fatan 'ya'yanta su zama likitoci idan suka girma.
"Ni dai zan so su zama likitoci, amma ban san me za su zaɓa ba bayan sun girma saboda kowa na da zaɓin shi idan ya girma.
"Sai dai zan faɗa musu su zama likitoci saboda an haife su manne da juna domin su ma su taimaki tagwaye da za a haifa a manne nan gaba," in ji ta.
Sai dai a yayin da Mrs. Ebiyenfa ke ganin ta aikata abun kunya sakamakon haihuwar tagwayen a manne, shi kuwa mahaifin tagwayen Mista Ebeleme Rafeal tunanin ɗawainiyar da ta yi ma sa sallama yake yi.
"A lokacin da matata ta haifi waɗannan tagwayen na ji wani iri. ji na yi me ya sa haka za ta faru da ni a waɗannan shekarun nawa sannan kuma gashi ni ba wani mai ido da kwalli ba ne amma yanzu ga 'ya'ya na a rabe godiya ta tabbata ga Allah," in ji shi.
An haifi tagwayen ne a ƙaramar hukumar Nembe ta jihar Bayelsa da ke kudancin Najeriya sannan aka kai su jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin ƙasar tun a watan Janairun wannan shekarar domin fiɗar.
Wannan shi ne karo na uku da cibiyar gwamnatin tarayya da ke Yola ta yi tiyatar rabon tagwaye da aka haifa manne da juna bayan wanda aka taɓa yi a shekara ta 2018.









