Matsalar fyaɗe: 'Yan Najeriya na so a hukunta mutanen da suka yi wa budurwa fyaɗe ta mutu a coci

uwavera omozuwa

Asalin hoton, uwavera omozuwa/facebook

Bayanan hoto, Burin Uwavera Omozuwa shi ne zama ma'aikaciyar jinya
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Matakin da rundunar 'yan sanda a jihar Edo da ke Najeriya ta dauka na yin baje-kolin mutanen da ake zargi da kashe wata ɗalibar Jami'ar Benin mai suna Uwaila Vera Omozuwa ya ja hankalin masu amfani da shafukan sada zumunta musamman Twitter.

Rundunar 'yan sandan ta gabatar da mutum shida da ta kama a gaban manema labarai ranar Laraba.

Wani bidiyo da wasu kafafen watsa labarai suka sa a shafukan sada zumunta, ya nuna yadda 'yan sandan a gaban ofishinsu suke yi wa mutanen tambayoyi.

Mutanen da ake zargin sun shaida wa 'yan jarida cewa wata mata mai suna Misis Mary Ade ta ba su naira miliyan ɗaya domin su aiwatar da kisan domin cimma wata buƙata ta tsafi.

Waɗanda ake zargin sun haɗa da Nelson Ogbebor da Akato Valentine da Misis Tina Samuel da Misis Mary Ade da Nosa Osabohien da Collins Ulegbe.

Sun bayyana cewa bayan an kammala yi wa Uwa fyaɗe, sun yi amfani da farin ƙyalle wurin goge mata jiki inda suka miƙa ƙyallen ga Misis Mary Ade.

Hakan ya yi matuƙar ɓata ran masu amfani da shafukan sada zumunta inda suka rinƙa yin zanga-zanga suka buƙaci a ƙwato wa Uwa haƙƙinta.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Me mutane ke cewa bayan kama waɗanda ake zargi?

Jama'a da dama a shafukan sada zumunta musamman Twitter na tofa albarkacin bakinsu kan wannan kamen da 'yan sandan Najeriya suka yi. Mutane na tattauna wannan batu a shafin Twitter da mau'du'in #JusticeForUwa

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Wannan cewa ya yi "kada wannan lamarin ya tsaya a kamen da aka yi, ya kamata a yi musu hukuncin da ya dace, wannan mugun abu ne mai ban takaici, ta ya bil adama za su yi haka".

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 3

Wannan kuma cewa ta yi "na ji daɗi da na ji labarin cewa waɗanda suka ci zarafin Uwa an kama su. Dole shari'a ta yi hukunci a kansu.

"Ina roƙon ubangiji ya ci gaba da ba 'yan uwanta da masoyanta haƙuri."

Kauce wa X, 4
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 4

Wannan cewa ta yi "a karon farko, ina murna da 'yan sandan Najeriya, amma duk da haka su tabbatar an yi adalci kan wannan lamari.

Waiwaye

A watan Mayu ne ɗalibar mai shekara 22 da ke nazarin ilimin ƙananan halittu ta je cocin Redeemed da ke kusa da jami'ar Benin domin yin karatu kamar yadda ta saba yi, inda aka je aka same ta yashe a kasa jina-jina.

An ce an rotse kan Uwavera ne da tukunyar sinadarin kashe wuta bayan an yi mata fyade.

Ƴar uwar marigayiyar, Judith Omozuwa ta shaida wa BBC cewa sai bayan kwana uku ne ta mutu a asibiti.

"An kira babata daga coci cewa mu je ba su san abin da ya faru ga 'yar uwata ba . Wata mace wadda ta samu 'yar uwar tawa ta ce ta same ta kwance cikin jini kuma an yayyaga sikyat da dan kamfanta," in ji ta.

Ta ƙara da cewa: "Sun yi mata fyade, don ba ta taba sanin ɗa namiji ba. Ina matukar son ganin an samu waɗanda suka yi mata fyade domin a hukunta su."

A wancan lokacin, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar ta Edo, DSP Chidi Nwabuzor ya shaida wa BBC cewa sun fara bincike don gano makasanta tun bayan da labarin yarinyar ya bazu a shafukan sada zumunta.

Shi kansa gwamnan jihar, Godwin Obseki ya umarci rundunar ƴan sandan jihar da ta gudanar da bincike da kuma hukunta duk wanda aka samu da hannu a al'amarin.

Wannan layi ne

'Mace ɗaya aka yi wa fyaɗe cikin kowacce awa biyar a Najeriya'

Nigerian Police IGP Mohammed Adamu

Asalin hoton, Nigeria Police force

Bayanan hoto, Mohammed Adamu ya ce zuwa yanzu an kama mutum 799 da ake zargi yayin da aka gudanar da bincike kan lamari 631 aka kuma gurfanar da su a kotu

Babban sufeton 'yan sandan Najeriya Mohammed Adamu ya ce mata 717 aka yi wa fyaɗe cikin wata biyar a Najeriya, daga watan Janairu zuwa watan Mayun 2020.

Mohammed Adamu ya ce an kama mutum 799 da ake zargi yayin da aka gudanar da bincike kan lamari 631 aka kuma gurfanar da su a kotu, sannan har yanzu ana ci gaba da bincike kan kamarin 52.

Shugaban 'yan sandan ya ce mai yiwuwa ne matakan takaita zirga-zirgar da aka sanya sakamakon annobar cutar korona ya taimaka wajen samun karuwar fyaɗe a sassan kasar.

"Mun fahimci cewa a yanzu saboda takaita zirga-zirga sakamaon Covid-19, mun samu karuwar yawan masu aikata fyade da cin zarafi. Muna so mutane su fahimci cewa dama can ana aikata wadannan laifuka, amma suna karuwa ne a yanzu.''

Mohammed Adamu ya bayar da tabbacin cewa hukumomin tsaro suna aiki don magance wadanda abubuwa, duk da cewa ba lallai mutane su san irin matakan da ake dauka ba.

Wannan layi ne

Me ke janyo fyaɗe?

Matsalar fyade a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Tsananin bukatar yin jima'i - Likitoci sun ce wannan matsala na faruwa ne sakamakon ciwon ƙwaƙwalwar da ke damun mutanen da ke aikata fyaɗe.

Dr Attahiru Muhammad Bello, wani likitan ƙwaƙwalwa ne a hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar Adamawa, kuma ya shaida wa BBC cewa matsalar gagaruma ce.

"Yawancin masu yi wa ƙananan yara fyaɗe suna fama da cutar da a Turance ake kira paraphilia, wato wata jarabar matuƙar bukatar yin jima'i, ko da kuwa da wani abu kamar ƙarfe ne ko kuma ƙananan yara."

Ya ce a kasashen da aka ci gaba ana sanya musu ido idan aka ga suna nuna irin wannan ɗabi'u tun suna yara ta yadda za a riƙa yi musu magani tare da da ba su shawarwari.

Taɓin ƙwaƙwalwa - Dr Shehu Saleh shugaban asibitin kula da masu lalular ƙwaƙwala da ke garin Kware a jihar sokoto ya ce matsalar taɓin ƙwaƙwalwa na daga cikin dalilan da ke sa wasu su aikata fyaɗe musamman wadanda ba za su iya bambance abu mai kyau da marar kyau ba, kamar waɗanda ke aikata sata ko fashi da makami.

"Duk za su iya aikata fyaɗe saboda ba su san cewa laifi ne suka aikata ba, saboda ƙwaƙwalwarsu ta juye."

Sai dai Likitan ya ce yawancin masu aikata fyaɗe dama ce suka samu tsakaninsu da waɗanda suke yi wa fyaɗen da kuma mugun halin da ke ransu.

Ya ce akwai hanyoyi da dama da mutum zai bi ya biya bukatarsa ta samun gamsuwa amma saboda mugun halin da ke ransu ke sa su aikata yin fyaɗe.

Likitan ya ce fyaɗe na iya jefa yaran da aka yi wa cikin damuwa kan mugun abin da aka aikata masu, wanda zai iya shafar ƙwaƙwalwarsu.

"Babban matsalar fyade shi ne yaran da aka yi wa fyaden, yana janyo masu taɓin hankali har ta kai su ma suna yi wa wasu fyaden," in shi Dr Shehu Saleh.

Karin labarai da za ku so ku karanta: