Harin Masallaci a Christchurch: Brenton Tarrant zai shafe rayuwarsa a kurkuku
Wata kotu a New Zealand ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga maharin da ya kashe musulmi masallata 51 yayin da suke ibada a Chrischurch.
Alkalin kotun Cameron Mander, ya ce Brenton Tarrant, ya shirya sosai kafin kai harin kan wasu masallatai biyu.
Ya ce zuciyar sa ta kekashe, kana bai nuna tausayi ko da na sanin abin da ya aikata ba.

Asalin hoton, Getty Images
Wannan dai shine karo na farko da aka yanke hukuncin daurin rai da rai ba tare da bada wata dama ba a New Zealand.
Kafin yake hukuncin dangin wadanda ya kashe sun bukaci kotu ta yi masa hukunci mafi tsanani.

Firaministar New Zealand Jacinda Ardern, ta yi maraba da hukuncin da aka yankewa maharin da ya hallaka masallata a wasu masallatai a kasar, in da tace maharin ya cancanci ya karasa rayuwarsa a kurkuku, tana mai fatan daina sake jin duriyarsa har abadan abada.

Asalin hoton, EPA
Ta kuma yabawa dangin wadanda suka mutu saboda hakurin da suka nuna tsawon lokaci har zuwa yanzu da aka yanke hukunci.
An fara kai wa masallacin Al Noor mosque hari ne wanda yake tsakiyar birnin Christchurch.
Wasu da suka shaida al'amarin sun ce sun rika gudu don neman tsira da rayuwarsu, a dai-dai lokacin da suka ga wasu mutane suna fitowa daga cikin masallacin jina-jina.










