An tabbatar da Joe Biden a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa

Asalin hoton, Reuters
A hukumance an tabbatar da Joe Biden a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasar na jam'iyyar Dimokrat a zaɓen Amurka da za a yi cikin watan Nuwamba.
Matakin na zuwa a rana ta biyu ta babban taron ƙasa da ake gudanarwa ta hanyar intanet na babbar jam'iyyar mai adawa.
An gabatar da shi ne ta hanyar jawaban da aka naɗa a bidiyo daga jihohin da ke faɗin ƙasar.
Ga bayanin yadda ta kasance lokacin da ake bayyana Joe Biden a matsayin ɗan takarar
Mai gabatar da masu jawabi ya fara da "Godiya ga dukkan daliget ɗinmu.
Ina mai farin cikin ba da sanarwar cewa an zaɓi Mataimakin shugaban ƙasa Joe Biden a hukumance don zama ɗan takararmu na shugaban Amurka a jam'iyyar Dimokrat.
A nan ina gayyatar Mataimakin Shugaban ƙasa Biden ya gabatar da jawabinsa na amincewa..."
A nasa ɓangare kuma Mista Joe Biden ya ce: "Na gode maka ƙwarai, ƙwarai da gaske.
Har cikin zuciyata. Ina gode muku gaba ɗaya. Babu wani abu a duniya da ya fi wannan karimci a gare ni, da ma iyalina.
Kuma za mu haɗu da ku ranar Alhamis. Na gode, na gode, na gode."











