Ayodhya Ram Mandir: Firaminista Modi ya jagoranci gina sabon wurin ibada

Devotees walk past pillars in the city of Ayodhya, India

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wasu turakan da za a kafa a filin da za a gina wurin ibadar na ƴan Hindu
An wallafa

Firaministan Indiya Narendra Modi ya jagoranci aza harsashin gina wani sabon wurin ibada na mabiya addinin Hindu a birnin Ayodhya a arewacin ƙasar.

Wannan ne wurin da aka daɗe ana tafka rikici tsakanin mabiya addinin Hindu da Musulmi - waɗanda kowannensu ke cewa shi ne ya mallaki wurin.

A 1992 'ƴan Hindu suka rusa wani tsohon masallacin da aka gina a ƙarni na 16, bayan da suka ce da ma wurin ibadar su ne aka gina Masallacin a kai.

Kotun Ƙolin ƙasar ta miƙa wa mabiya addinin Hindun wurin a bara wanda ya kawo ƙarshen rikicin da aka shafe gomman shekaru ana tafkawa a gaban kotuna.

Kotun ta ba Musulmin wani filin na dabam a cikin birnin domin su gina nasu masallacin.

Devotees lighting earthen lamps in Ayodhya
Bayanan hoto, Mabiya addinin Hindu na shirye-shiryen bikin sake gina wurin ibadar.

Yadda aka shirya bikin

Mista Modi ya shirya aza wani bulo na azurfa a wurin da za a gina wani daki na musamman, inda dubun dubatan mabiya za su kalli bikin a manyan akwatunan talabijin da aka kafa a fadin birnin.

Tashoshin talabijin na Indiya kuwa za su shafe yinin suna nuna bikin.

Rahotanni masu yawa na cewa mabiya addinin Hindun na ta aikawa da zinare da azurfa da za a hada wajen gina wurin ibadar. 'Yan sanda kuma sun ce an ba su umarnin kare kayan masu matukar daraja daga barayi.

Za a rubuta "Shri Ram (wato ubangiji Ram) a jikin tubali kimanin 20,000 da mabiya addinin Hindun suka bayar gudunmawa a shekarun da suka gabata domin gina wurin ibadar, kamar yadda jaridar Times ta Indiya ta wallafa.

A skyline view of Ayodyha, India

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Hoton birnin Ayodhya a arewacin Indiya

Mabiya addinin Hindu sun daɗe suna cewa an gina masallacin mai suna Babri ne a kan tsohon wurin ibadarsu a zamanin da Musulmai suka kai hari a yankin kuma suka mulke shi na wani lokaci.

Musulmai kuwa sun ce har zuwa 1949 sun riƙa yin salloli a masallacin kafin wasu ƴan Hindu suka kafa wasu gunkin Ram a cikin masallacin kuma suka fara bautawa gumaka.

Gomman shekaru sun shuɗe ana shari'a a kotu kan wanda ke da ikon mallakar wurin.

A devotee in Ayodhya

Asalin hoton, Ankit Srinivas

Bayanan hoto, Firaminista Modi zai aza harsashin gina sabon wurin ibada na Ayodhya