Mayaƙan IS da aka kora daga Syria 'suna tunkarar Afirka da Asia'

IS militants in Anbar province (2014)

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An fatattaki ƙungiyar IS ne bayan wani rikici da ya shafe tsawon lokaci a ƙasashen Iraƙi da Siriya
An wallafa

Wani binciken ƙwararru daga Burtaniya ya yi gargaɗin cewa mayaƙan ƙungiyar IS na sake gamuwa a sauran sassan duniya, bayan an yi galaba kan 'yan ta-da-ƙayar-bayan a yankin Gabas ta Tsakiya.

Rahoton na Jami'ar Kings College London da haɗin gwiwar Cibiyar Nazarin harkokin aikin soja a Duniya ya ce akwai shaidar da ke nuna cewa tsoffin masu iƙirarin jihadi mai yiwuwa suna tunkarar wuraren da ke fama da rikice-rikice.

A cewar nazarin dai, 'yan ta-da-ƙayar-bayan na nufar yankin Kudu maso gabashin Asiya da kuma Afirka, lamarin da ya sabunta barazanar tsaro ga ƙasashen duniya.

Masu binciken sun nuna cewa wasu daga cikin alhakin wannan al'amari ya rataya ne a wuyan gwamnatocin ƙasashen Yamma.

Sun dai ce ƙasashen na Yamma sun gaza magance matsalar 'yan ƙasashensu waɗanda kan niƙi-gari zuwa wata ƙsa don shiga ƙungiyar IS.

Lamarin da kan sa a wasu lokuta, su ƙare a gidajen yarin ƙasashen Siriya da Iraƙi masu raunin tsaro.