Imran Khan: An yi wa firaministan Pakistan rubdugu don ya ce Osama Bin Laden ya yi shahada

Asalin hoton, AFP
'Yan majalisar dokokin Pakistan na jam'iyyar hamayya sun yi wa Firaiministan kasar Imran Khan rubdugu bayan da ya shaida wa majalisar cewa Osama Bin Laden shahada ya yi sakamakon kashe shi da Amurka ta yi.
An kashe Bin Laden ne, wanda shi ya shirya kai harin watan Satumban 2011, a lokacin da dakarun Amurka na musamman suka kai samame maboyarsa a birinin Abbottabad na Pakistan.
Ba a sanar da Pakistan batun kai samamen ba kafin a yi.
"Ba zan taba manta taskun da 'yan Pakistan suka ji ba a lokacin da Amurkawa suka shigo Abbottabad suka kashe Osama Bin Laden, ya yi shahada a hannunsu," a cewar Khan.
Khan ya yi amfani da kalmar "shaheed" - wata kalmar Larabci da ke nufin wanda ya yi shahada.
Jagoran 'yan hamayya kuma tsohon Ministan Harkokin Wajen Pakistan Khawaja Asif ya soki Mr Khan, inda ya bayyana Bin Laden "a matsayin babba dan ta'adda".
"Ya lalata kasata, sannan kuma Khan yana kiransa Shahidi,'' kamar yadda Mr Asif ya fada a zauren majalisar.
Shi kuwa Bilawal Bhutto Zardari, wanda jam'iyyarsa ta Pakistan Peoples Party ce ke mulkin kasar a lokacin da aka kashe Bin Laden, ya soki firai ministan ne da goyon bayan tsattsaurar akida.
Meena Gabeena, wata fitacciyar mai fafutuka a Pakistani, ta rubuta a Twitter cewa: "Musulmai a ko ina a fadin duniya suna shiga tasku kan wariyar da ake nuna musu sakamakon ayyukan ta'addanci da ake yi da sunan addininsu sannan yanzu Firaminista ya sake munana lamarin ta hanyar kiran Osama Bin Laden shahidin Musulinci!''
Kalaman Mista Khan na zuwa ne a yayin da ofishin harkokin wajen Pakistan ya ki karbar wani rahoto daga ma'aikatar harkokin cikin gida ta Amurka da ke zargin Pakistan da ci gaba da zama mafakar kungiyoyin 'yan ta'adda.
"A yayin da rahoton ya ce kimar al-Qaeda na matukar raguwa a yankin, ya ki ya bayyana rawar da Pakistan ke takawa wajen kashe karfin al-Qaeda, wanda hakan ya rage barazanar da a da kungiyar ta'addancin ke yi wa duniya,'' a cewar ofishin harkokin wajen Pakistan din.

Asalin hoton, AFP
A baya an sha sukar Mr Khan, wanda tsohon dan wasan kurket, da cewa yana yawan nuna tausayi ga Taliban, har ma 'yan adawa suka yi masa lakani da "Taliban Khan".
Biyo bayan kalaman nasa masu cike da ce-ce-ku-ce kan Bin Laden a ranar Alhamis, wani tsohon dan majalisar dattawan kasar kuma tsohon shugaban hukumar kare hakkin dan adam ta Pakistan Afrasiab Khatak, ya wallafa sako a tuwita, inda ya ce an firaministan ya hau mulki ne saboda ya aiwatar da ''Shirin Taliban''.
A wata hira da aka taba yi da shi a talabijin shekara hudu da suka gabata, Mr Khan ya ki kiran Bin Laden dan ta'adda duk da matsa masa lamba da dan jaridar ya yi kan tambayar.

Sharhi: M Ilyas Khan, BBC News, Islamabad
Imran Khan ya kira Osama Bin Laden shahidi ne ba wai don yana da wata akida ko ra'ayi kan harin 9/11 ba, amma ya yi hakan ne saboda akidar siyasa.
Duniya ta jima a cikin siyasar harin 9/11, amma har yanzu masu sharhi na kallon ta'addancin da sunan Musulunci a matsayin wani makami da sojojin Pakistan masu karfi ke amfani da shi wajen cimma manufarsu a Indiya da Afhganistan.
Har yanzu 'yan ta'addan na girmama Bin Laden da sauran manyan al-Qaeda da Taliban na baya, kuma ana amfani da sunansu wajen shigar da mutane cikin kungiyoyin. Don haka duk wani kokari na durkusar da matsayin Bin Laden za a yi yaki da shi.
Masu sukar Mr Khan na yi masa kallon wani wanda ke kusa da sojoji - wani dan korensu da suka dora shi a kujerar mulki a 2018 a wani zabe da ake zargin sojojin sun tafka magudi.
Ana ganin kalamansa na ranar Alhamis a matsyain da gangan. Wasu da yawa sun lura da cewa da farko ya yi amfani da kalmar kisa a kan Bin Laden, sai kuma ya dakata ya gyara da cewa ya yi shahada.











