Buhari ya ce Giadom ne shugaban riko na jam'iyyar APC

Asalin hoton, Victor Giadom/twitter
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce Victor Giadom ne shugaban riko na jam'iyyar APC na kasar.
Mai taimaka wa shugaban kan harkokin yada labarai Garba Shehu ne ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter ranar Laraba da yamma.
Ya ce shugaban ya dauki wannan mataki ne sakamakon shawarwarin masana shari'a kan halin da jam'iyyar take ciki.
Sanarwar ta ce Shugaba Buhari zai halarci taron da Victor Giadom ya kira ranar Alhamis, wanda za a gudanar ta bidiyo, tare da sa ran cewa gwamnonin jam'iyyar da shugabannin majalisar dokoki na APC za su halarci taron.
Sanarwar ta fadar shugaban kasa ta yi kira ga kafofin watsa labarai su guji yada rikice-rikicen da ake yada cewa jam'iyyar APC ta na da su, sannan su kiyayi ba da dama ga mutane suna fadar son ransu kan lamarin shugabancin jam'iyyar.
Matsayar ta Shugaba Buhari na zuwa ne kwanaki biyu bayan wasu gwanmnonin jam'iyyar ta APC suka gana da shi.
Gwamnonin su ne Atiku Bagudu na jihar Kebbi, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin jam'iyyar APC, da gwamnan jihar Platue Simon Lalong shugaban kungiyar gwamnonin arewacin Najeriya da gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar.
Gwamnonin sun je ne domin gabatar da matsayarsu ga shugaban kasa kan rikicin jam'iyyar ta APC.
Jam'iyyar ta APC ta fada cikin rikicin shugabanci ne bayan wata kotu a Abuja ta sauke Adams Oshiomhole daga shugabancin jam'iyyar.
Bayan sauke shi ne mataimakin sakataren jam'iyyar Victor Giadom ya yi da'awar cewa shi ne ya kamata ya zama shugaban jam'iyyar kasancewar sa ya fito ne daga yankin da Adams Oshiomhole ya fito, kamar yadda kundin tsarin mulkin jam'iyyar APC ya nuna.










