Coronavirus: Hotunan Sallar Juma'a a Abuja karon farko bayan wata biyu

An wallafa

Bayan shafe fiye da wata biyu masallatan Juma'a na kulle, mazauna birnin Abuja - Babban Birnin Tarayyar Najeriya - sun halarci jam'in sallar a karon farko.

Ga wasu zaɓaɓɓun hotuna na yadda sallar ta gudana a wasu masallatan birnin:

Shugaba Buhari

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Bayanan hoto, Shugaba Muhammadu Buhari ya gudanar da tasa sallar Juma'ar a masallacin Fadar Gwamnati ta Aso Rock Villa
Shugaba Buhari

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Bayanan hoto, Kamar yadda ake gani, Buhari ya yi sallar ne da wasu daga cikin muƙarrabansa
Masallacin Juma'a na Bannex da ke Abuja
Bayanan hoto, Umar Rufa'i, na'ibin limamin Masallacin Bannex, shi ne ya jagoranci Juma'a a masallacin da ke Wuse II a Abuja
Masallacin Juma'a na Bannex da ke Abuja
Bayanan hoto, Huɗubar da limamin ya yi ta mayar da hankali ne kan annobar korona, inda ya yi roƙon Allah ya kawo karshenta da kuma kiran mutane su ci gaba da kiyayewa
Sallar Juma'a a Abuja

Asalin hoton, BBC

Bayanan hoto, Ɗumbin al'ummar Musulmi sun halarci sallar Juma'a a Masallacin Juma'a na Zone 3 da ke Abuja
Masallacin Juma'a na Zone 3 da ke Abuja
Bayanan hoto, Wasu daga cikin masallatan sun shaida wa BBC farin cikinsu da buɗe masallacin
Masallacin Juma'a na Bannex da ke Abuja

Asalin hoton, BBC

Bayanan hoto, An ɗauki wasu matakan kariya a Masallacin Bannex

Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka.