Coronavirus: Kulawa ta musamman da manyan kalmomi da aka yi bayani

Jargon buster
An wallafa

Annobar korona ta sa an kirkiri wasu sabbin kalmomi da kuma bayanan da muke amfani da su a kullum, kama daga bayar da tazara da kuma garkuwar jiki mai karfi. Amma me wadannan duka suke nufi?

Yi amfani da ma'aunin fassararmu domin ganin ma'anarsu.

Ku sabunta intanet dinku

Fassarar kalmomin coronavirus

Me duka kalmomin ke nufi?

Tsallaka zuwa cikakken labari
  • Gwajin garkuwar jikin mutum

    Gwajin da ke nuna ko mutum ya kamu da cutar korona kuma a yanzu garkuwar jikinsa na da dan karfi. Gwajin na nuna kwayoyin garkuwar jikin mutum a cikin jini, wadanda jiki ke samarwa da suke yakar cututtuka.

  • Wanda ba ya nuna alamun cutar (Asymptomatic)

    Wanda ke dauke da cutar amma ba ya nuna alamun da take haddasawa. Wasu bincike sun nuna cewa wasu mutanen kan kamu da cutar korona amma ba sa nuna alamunta kwata-kwata, kamar tari mai naci da zazzabi mai zafi.

  • Cutar korona

    Daya daga cikin dangogin kwayar cutar virus da ke jawo rashin lafiya mai tsanani ko saisa-saisa ga 'yan adam da kuma dabbobi. Kwayar korona da a halin yanzu ta gallabi duniya ita ce ke jawo cutar Covid-19. Murar da aka saba yi da tari na daga cikin dangogin kwayar cutar korona.

  • Covid-19

    An fara gano kwayar cutar korona a Wuhan da ke China, a karshen shekarar 2019. Ta fi shafar huhu.

  • Matakan da ake dauka na kariya daga cutar na tasiri

    Domin rage yawan yaduwar cutar, an yi yadda yawan da aka kai na wadanda suka kamu ba zai rika karuwa ba, ta yadda yawan masu cutar ba zai fi karfin yawan asibitoci ba.

  • Mura

    Kwayar cutar virus da ke haddasa mura mai tsanani ga mutane da dabbobi, ta kan kuma iya haddasa annoba.

  • Yawancin mutane na da garkuwa da cutar

    Yadda yaduwar cutar ya ragu bayan da mutane da dama daga cikin al'umma suka kamu da ita.

  • Samun kariya

    Mutumin da jikinsa zai iya jure wata cuta ko ma ya yake ta, za a iya cewa yana da kariyar cutar kenan. Da zarar mutum ya warke daga cutar da kwayar corona ta jawo, ga misali Covid-19, ana sa ran ba zai iya sake kamuwa da ita ba na tsawon wani lokaci.

  • Tsawon lokacin da kwayar cutar ke kyankyashewa

    Lokaci tsakanin kamuwa da cuta da kuma fara nuna alamunta.

  • Kulle

    Dokar takaita zirga-zirgar yau da kullum, inda ake rufe wuraren tarywar jama'a sannan a umarci mutane su zauna a gida. An sanya dokar kulle a kasashe da dama a wani bangare na daukar kwakkwaran matakin hana yaduwar cutar korona.

  • Barkewar cutar

    Karuwar masu kamuwa da cuta da yaduwarta a wurare daban-daban.

  • Annoba

    Annobar wata cuta da ke yaduwa da sauri a kasashe da dama a lokaci guda.

  • Killacewa

    Killace mutanen da suka kamu da wata cuta mai yaduwa don gudun kara bazuwarta.

  • Cutar Sars (nau'in cutar numfashi ta sars)

    Wata cutar numfashi dangin cutar korona da aka yi fama da ita a yankin Asiya a shekarar 2003.

  • Killace kai

    Zama a gida da daina duk wata cudanya da sauran mutane, da nufin kare yaduwar cutar.

  • Nesa-nesa da juna

    Daina mu'amala da mutane da nufin rage yaduwar cutar. Gwamnati ta shawarci a daina ziyartar abokai da dangi sai dai wadanda dama tare kuke zaune, da yin aiki daga gida da kuma daina hawa abin hawa na haya.

  • Dokar ta baci

    Matakan da gwamnati ta dauka don hana zirga-zirgar yau da kullum a yayin da take kokarin shawo kan lamarin. Hakan ya hada da rufe makarantu a wuraren aiki da takaita shiga da fitar jama'a da ma baza sojoji don taimaka wa sauran ma'aikatan agaji.

  • Alamomi

    Duk wata alamar rashin lafiya, da garkuwar jiki ke jawowa a kokarin da take na yakar cutar. Manyan alamun cutar korona su ne zazzabi da tari mai zafi da wahala wajen shan numfashi.

  • Riga-kafi

    Ba da magani da ke jawo jiki ya samar da kwayoyin gwajin garkuwar jiki mutum, wadanda ke yaki da cutar, tare da ba da garkuwar da za ta yaki wasu cututtukan a gaba.

  • Na'urar Ventilator

    Wata na'ura da ke taimakawa wajen shan numfashi idan cutar ta jawo huhu ya daina aiki.

  • Virus/bairos

    Wata 'yar karamar kwayar cuta da ke shiga cikin kwayoyin halittar duk wani abu mai rai. Bairos ka iya jawo kwayoyin halittar su mutu ko ta shafi sinadaran da jiki ke samarwa su daina aiki, hakan kuma ya jawo rashin lafiya.

Cigaban labarin na kasa

Manyan kalmomin annobar

Covid-19

Kwayar cutar da ake kamuwa da ita ta dalilin cutar korona wadda aka fara samu a birin Wuhan da ke China a karshen 2019. Babbar illar da take yi shi ne ta hana huhu aikinsa.

Hawa da saukar cutar

Masana lafiya na amfani da zane wajen nuna hawa da sauka na sabbin masu dauke da cutar. Idan mutane da dama sun kamu da cutar cikin kankanin lokaci, zanen zai yi tsiri nan da nan ya yi kamar tsayin dutse. Haka kuma, daukar matakan rage yaduwar cutar na dogon lokaci na nufi "Shawo kanta". Wannan ya saukaka wa tsarin lafiya wajen fama da cutar.

Kulle

Hana zirga-zirga, inda ake kulle don wasu gine-gine tare da umartar mutane su zauna a gida. An sanya dokar kulle a kasashe da dama a matsayin yunkurin shawo kan yaduwar cutar korona.

Annoba

Annoba wata mummunar cuta ce da ke yaduwa zuwa kasashen duniya cikin gaggawa.

Killace kai

Zama wuri daya tare da kauncewa duk wata hulda da mutane da nufin hana yaduwar cutar.

Ba da tazara

Yin nesa-nesa da sauran mutane da nufin takaita yaduwar cutar. Gwamnati na ba da shawarar kar a ziyarci abokai ko 'yan uwa ban da wadanda ake rayuwa tare da su waje daya, za a iya aiki daga gida kuma a nisanci wuraren ababan hawa na jama.

Kwayar Cuta

Wata 'yar karamar halitta ce da ke samar da irinta a cikin jikin abin halitta. Kwayoyoin cuta na kashe kwayoyin halittar jikin wanda ta kama tare da rikita tsarin aikinsu na yau da kullum, kwayoyin cuta ne ke jan haka.

Karin bayani kan coronavirus
Karin bayani kan coronavirus