Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Kulawa ta musamman da manyan kalmomi da aka yi bayani
Annobar korona ta sa an kirkiri wasu sabbin kalmomi da kuma bayanan da muke amfani da su a kullum, kama daga bayar da tazara da kuma garkuwar jiki mai karfi. Amma me wadannan duka suke nufi?
Yi amfani da ma'aunin fassararmu domin ganin ma'anarsu.
Manyan kalmomin annobar
Covid-19
Kwayar cutar da ake kamuwa da ita ta dalilin cutar korona wadda aka fara samu a birin Wuhan da ke China a karshen 2019. Babbar illar da take yi shi ne ta hana huhu aikinsa.
Hawa da saukar cutar
Masana lafiya na amfani da zane wajen nuna hawa da sauka na sabbin masu dauke da cutar. Idan mutane da dama sun kamu da cutar cikin kankanin lokaci, zanen zai yi tsiri nan da nan ya yi kamar tsayin dutse. Haka kuma, daukar matakan rage yaduwar cutar na dogon lokaci na nufi "Shawo kanta". Wannan ya saukaka wa tsarin lafiya wajen fama da cutar.
Kulle
Hana zirga-zirga, inda ake kulle don wasu gine-gine tare da umartar mutane su zauna a gida. An sanya dokar kulle a kasashe da dama a matsayin yunkurin shawo kan yaduwar cutar korona.
Annoba
Annoba wata mummunar cuta ce da ke yaduwa zuwa kasashen duniya cikin gaggawa.
Killace kai
Zama wuri daya tare da kauncewa duk wata hulda da mutane da nufin hana yaduwar cutar.
Ba da tazara
Yin nesa-nesa da sauran mutane da nufin takaita yaduwar cutar. Gwamnati na ba da shawarar kar a ziyarci abokai ko 'yan uwa ban da wadanda ake rayuwa tare da su waje daya, za a iya aiki daga gida kuma a nisanci wuraren ababan hawa na jama.
Kwayar Cuta
Wata 'yar karamar halitta ce da ke samar da irinta a cikin jikin abin halitta. Kwayoyoin cuta na kashe kwayoyin halittar jikin wanda ta kama tare da rikita tsarin aikinsu na yau da kullum, kwayoyin cuta ne ke jan haka.