Coronavirus: Ana tilasta mana biyan kudin killacewa - Ɗaliban Najeriya

Daliban Najeriya da ke karatu a wasu kasashen waje na kokawa a kan kudin killace su da aka ce sai sun biya

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Yayin da Najeriya ke ci gaba da kwaso 'yan kasar da suka makale a kasashen waje saboda annobar korona, wasu 'yan kasar na kokawa da yawan kudin da aka ce su biya domin dauko su zuwa gida.

Daga cikin masu korafin akwai dalibai dake a kasar Indiya wadanda ke korafin cewa an bukaci su biya kudaden da suke ganin sun yi matukar yawa.

Wasu daga cikin daliban da BBC ta tattauna da su ta waya, sun ce ofishin jakadancin Najeriya d ake Indiyan ya aike musu da wata takarda inda aka bukace su da su biya kudaden tikitin jirgi da kuma kudaden da za a killacesu idan sun koma Najeriyar.

Bashir Ahmad Aliyu, na daga cikin daliban da ke karatu a kasar ya kuma shaida wa BBC cewa, bisa wannan tsarin, kowanne dalibi da za a dawo dashi gida Najeriya sai ya biya naira dubu 568, 100, baya ga kudin killacewa kuma.

Dalibin ya ce " Bayan daliban sun yarda har sun tura kudadensu domin a fara shirin dawo da su kasarsu Najeriya, sai ga kuma wata takarda ta fito ance wai duk wanda za a debo shi zai biyawa kansa kudin killace shi da za a yi idan sun dawo Najeriyar".

Ya ce, " Kudin killacewar da zamu biya sun kai naira dubu 297,600, abin haushin shi ne duk wanda bai biya wannan kudi na killacewa ba, to ko da ya biya kudin tikitinsa ba za a dauko shi daga Indiyan ba".

Bashir Ahmad ya ce, duk da haka kuma, gwamnatin kasar Indiyan na yi musu gwajin cutar korona inda ake basu shaidar cewa mutum na da cutar ko kuma akasin hakan tun kafinma a dauko su daga can.

To amma kuma koda mutum ya biya kudin jirgi kuma an masa gwajin cutar kuma bashi da ita, in dai har bai biya kudin killacewa ba, to babu shi a wadanda za a mayar gida Najeriya.

Yawancin daliban dake karatu a Indiyan da BBC ta zanta dasu ta waya sun ce a matsayinsu na dalibai kamata ya yi Najeriya ta tallafa musu saboda duk guzurinsu sun kare.

Kan wannan batu, BBC ba tayi kasa a gwiwa ba domin sai da ta tuntubi wani jami'i a ofishin jakadancin Najeriya da ke Indiya, amma ya ce bashi da izinin cewa komai game da korafin daliban.

Karin bayani kan coronavirus