Muna yi wa almajirai gwaji kafin mu kai su garuruwansu — Nasarawa

Asalin hoton, Leadership Newspaper
Gwamnatin jihar Nasarawa ta bi sahun wasu jihohin arewacin Najeriya wajen mayar da almajirai jihohinsu na asali a wani mataki na dakile yaduwar cutar korona.
Almajiran kimanin 800 ne jahar ta tisa keyarsu zuwa jihohinsu a ranar Lahadi, 3 ga watan Afirilu, 2020 wadanda ta ce sune kashin farko na dubban almajiran da za ta mayar.
Mai magana da yawun gwamnan jihar Malam Yakubu Lamai, ya shaida wa BBC cewa kashin farko na almajiran 'yan kasa da shekara 10 ne, kuma an mayar da su ne jihohin Jigawa da Kaduna Taraba da Plateau da kuma Gombe.
Ya ce da sannu a hankali za su mayar da almajirai fiye da dubu ashirin jihohinsu na asali.
Mai magana da yawun gwamnan ya ce, dama mayar da almajiran garuruwansu na asali na cikin tsarin gwamnatin tun kafin ma a samu bullar wannan annoba ta korona.
Ya ce " Mu a nan jihar Nasarawa tsarinmu na mayar da almajiran ya fita daban da na sauran jihohi domin mu sai dai muka yi wa dukkan almajiran da muka mayar din gwajin cutar korona muka tabbatar ba su da ita sannan aka mai da su garurunsu".
Malam Yakubu Lamai, ya ce bayan nan ma sai da aka tantance su aka dauki hotunansu sannan aka tabbatar da inda za a kai su.
Ya ce" Mu a namu tsarinma dukkan almajiran da zamu kai garuruwan nasu har kauyukansu muke kai su, kuma mun basu abinci, sannan kowannensu sai da muka bashi takunkumin rufe fuska suka sanya".
Sannan kuma akwai kudi da gwamnati ta ba wa kowanne almajiri kafin a mayar da shi gida, kai hatta su kansu malaman da zasu kai almajiran an basu alawus inji Malam Yakubu Lamai.

Mai magana da yawun gwamnan ya ce, dalilinsu na mayar da su kai tsaye zuwa garurunsu ba a damkasu a hannun gwamnatocin jihohinsu ba, saboda na farko an yi musu gwaji kuma malamansu sun san garin kowa.
Ya ce, nan bada jimawa ba suke sa ran kammala kai dukkan almajiran fiye da dubu ashirin zuwa garuruwansu na asali.
Jihar Nasarawa dai ba itace jihar farko a Najeriya da ta fara mayar da almajirai garuruwansu na asali ba saboda gudun yaduwar cutar korona.
Jihohi da dama kamar Kano da Katsina sun dauki irin wannan mataki.











