Coranavirus: Watakila a tsawaita dokar hana fita a Abuja da Lagos

Shugaba Buhari da kwamitinsa na yaki da coronavirus

Asalin hoton, @PTFCOVID19

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Gwamnatin Najeriya ta ce tana duba yiyuwar tsawaita dokar hana fita a biranen Abuja da Legas da kuma Ogun saboda yadda ake kara samun yaduwar cutar coranavirus a kasar.

A ranar 29 ga watan Maris ne a jawabinsa ga 'yan kasa, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanar da kafa dokar hana fita na tsawon mako biyu a biranen guda uku domin dakile yaduwar cutar coronavirus a kasar.

Sakataren gwamnatin Tarayya kuma shugaban kwamitin shugaban kasa kan Covid 19, Boss Mustapha, a lokacin da yake bayani a Abuja kan halin da ake ciki a ranar juma'a ya ce, akwai yiyuwar tsawaita dokar hana fita wacce za ta kawo karshe a ranar Lahadi domin dakile yaduwar cutar.

Ya kuma ce akwai yiyuwar dokar za ta shafi karin wasu jihohi da cutar ta shafa baya ga Abuja da Legas da kuma Ogun.

Ya kara da cewa tawagarsa ta sanar da Buhari kan halin da ake ciki kawo yanzu, "kuma hakkin shugaban ne ya yanke shawara kan dacewar tsawaita dokar hana fita ko kuma aa."

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Karin bayani kan coronavirus
Karin bayani kan coronavirus

Zuwa yanzu mutum 305 suka kamu da coronavirus a Najeriya, yayin da 58 suka warke daga cikinsu. Cutar kuma kawo yanzu ta kashe mutum bakwai a Najeriya.

Ana ta kuma samun bullar cutar a sauran jihohi Najeriya inda yanzu ta bulla a jihohin Najeriya 19.

Jihar Legas inda cutar ta fara bulla a Najeriya ce ta fi yawan masu dauke da ita, sai kuma Abuja inda mutum 56 suka kamu.