Coronavirus: Tallafin biloniya dan China Jack Ma, ya iso Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
A ranar Talata ne jirgin sama na dakon kaya na Ethiopia ya sauka a Legas a Najeriya, inda ya kawo kayan da wani hamshakin mai arziki dan kasar China kuma mamallakin Gidauniyar Jack Ma, ya bai wa nahiyar Afirka tallafi na amfanin asibiti da suka shafi cutar Covid-19.
A ranar 16 ga watan Maris ne miliyoniyan ya sanar da tallafin a shafinsa na Twitter, a yayin da kasashen duniya da dama ke ci gaba da fafutukar hana yaduwar cutar.
Kayan sun hada da jaka 20,000 ga kowace kasa a Afirka wacce ta kunshi kayayyakin jinyar masu coronavirus da suka hada da takunkumin rufe fuska 100,000 da rigunan da ma'aikatan lafiya ke sa wa don kare kansu da sauran kayan da ake amfani da su wajen kula da masu cutar.
Jaridar intanet ta BusinessDay ce ta sanar da isar kayayyakin na Najeriya a ranar Talata da misalin karfe 3.20.


Dama tun a ranar Litinin da daddare kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Ethiopian Airlines ya sanar da tashin jirgin dakon kayan daga Addis Ababa zuwa kasashen Afirka don isar da su.
Tun da fari gidauniyar, ta ce Afirka za ta iya kare kanta daga coronavirus idan ta dauki mataki.
Ta ce: "Ba za mu iya kawar da kanmu daga hadarin da Afirka ke fuskanta ba, mu dauka cewa wannan nahiya mai mutum biliyan 1.3 za ta tsira a wannan iftila'i ba.
"Duniya ba za ta zuba ido ta ga mummunan abin da zai iya faruwa a Afirka ba kan wannan annoba ta Covid-19.
"Za mu iya daukar matakan kariya yanzu mu kuma shirya kafin lokacin faruwar wani abu, saboda Afirka za ta iya amfana da koyon darussa daga wasu kasashen da bala'in ya shafa."
Kazalika Gidauniyar ta Jack Ma ta ce nan ba da dadewa ba za ta fara aiki da cibiyoyin lafiya a Afirka don ba su horo ta intanet, na yadda ake kula da masu jinyar cutar Covid-19.
A jumlace Afirka za ta samu kayayyakin har miliyan 1.1 da suka kunshi takunkumin fuska miliyan shida da rigunan da ma'aikatan lafiya ke sa wa don kare kansu 60,000 da gilashin rufe fuska, kuma za a kai kayan birnin Addis Ababa na kasar Habasha ne.
Firai Ministan Habasha Abiy Ahmed Ali ne zai jagoranci rarraba kayayyakin tare da aike wa sauran kasashen.
Gidauniyar Jack Ma ta ce wannan annoba tana kara yaduwa kuma tana wuce duk yadda aka tsammace ta.









