Buhari ya manta da 'yarmu - Mahaifiyar Leah Sharibu

Dangin Leah Sharibu

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Rebecca Sharibu mahaifiyar Leah Sharibu, ta ce gwamnatin Buharia a Najeriya ta kasa ceto 'yarsu matshiyar da Boko Haram ke rike da ita tun bayan sace ta daga garin Dapchi a 2018.

A wata hira da sashen Hausa na BBC, Rebecca Sharibu da ke Birtaniya don ganawa da Firaministan kasar ta ce tun da Buhari ya kira ta yi magana da shi watanni bakwai bayan dauke 'yarta, gwamnati ba ta sake tuntubarsu ba.

A ranar 19 ga Fabrairu Boko Haram ta sace 'yan matan makarantar Dapchi ciki har da Leah Sharibu lokacin da suke kwance a cikin dakunan kwanan dalibai.

Leah Sharibu ita ce daliba daya tilo da ta rage cikin 'yan mata 110 da 'yan Boko Haram suka sace a makarantar sakandaren Dapchi da ke jihar Yobe.

Yanzu shekaru biyu ke nan tun bayan da Boko Haram ta sace daliban Dapchi a jihar Yobe.

"Tun da aka dauke su a watan Fabrairu amma sai watan bakwai na yi magana da Buhari ya ce Leah za ta dawo ba da dadewa ba kuma bayan sati biyu ya kara turo ministocinsa guda uku suka jaddada alkawalinsa.

"Sun karfafa min guiwa, amma daga waccan rana ban sake jin komi daga gwamnati ba," in ji mahaifiyar Leah.

Ta kuma ce za ta kai kukanta ga Firaministan Birtaniya don tilastawa gwamnatin Najeriya kara himma wajen kubutar da 'yarta.

"Damuwa na kawai su yi kokari su fitar min da yarinyana. Mu 'yarmu muke so."

"Ina jin ba dadi amma yaya zan yi tun da karfi na ba zai iya ba, kuma gwamnati ba ta yi komi ba," in ji ta.

A watan Janairu rahotanni a Najeriya sun ce Leah Sharibu wadda yanzu shekarunta 17 ta samu ciki daga wani babban kwamandan Boko Haram da ya aure ta kuma suke zaune a wajen Najeriya.