Dalilai hudu da suka sa Trump ya tsira daga tsigewa

Lamba 94

Asalin hoton, Alamy

An wallafa

Bayan sauraron karar tsige Shugaba Trump da aka kwashe makwanni biyu ana yi a majalisar dattawan kasar, a yanzu an wanke shi daga dukkanin zarge-zarge biyu da ake yi masa.

Dama abin da aka yi tunanin zai faru kenan, amma yadda shari'ar ta kasance ne abin jan hankali game da al'amarin baki dayansa.

Ga wasu muhimman abubuwa hudu da suka yi karin haske akan wannan batu - da kuma abu na gaba da zai faru.

Getty Images
Farin jini a jam'iyyarsa

  • 94%'Yan Republican sun goyi bayan shugabansu fiye da ko yaushe

    Bayanai: Gallup

    Wanke shi da majalisar ta yi wata alama ce da ke nuna yadda shugaban ya yi fice a cikin takwarorinsa na 'yan Republican.

    Idan da ba a yi wannan tunanin ba kafin maganar ta je gaban majalisa, a yanzu, idan da an yi tunanin ba shi da goyon bayan 'yan jam'iyyarsa da masu fada aji a cikin ta, to yanzu lokaci ya yi da ya kamata a sauya tunani.

    Wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka yi ta nuna cewa Shugaba Trump na da goyon bayan 'yan jam'iyyarsa kwarai da gaske, ba kamar yadda wasu 'yan Democrat ke tunani ba.

    Domin kaso 94 cikin 100 na 'yan Republican sun yi na'am da rawar da yake takawa a matsayinsa na shugaban Amurka, kuma duk da haka, wadannan alkaluma na ci gaba da yin sama duk kuwa da kokarin sauke shi da aka yi.

    Wannan layi ne

    Ba a taba ganin irin haka ba a tarihin kasar, mutumin da ke cikin shekararsa ta uku da darewa karagar mulki, kaso 89 cikin 100i na yan jam'iyyarsa suka jinjinawa salon kamun ludayinsa, abin da ya yi ta ci gaba har zuwa wannan lokaci da ake kyautata zaton cewa zai sake yi wa jam'iyyar tasa takara.

    Hatta mutane irin Sanatar jihar Alaska Lisa Murwoksi da ta ce ba za ta yi kasassabar zaben shugaban kasar a zaben 2016 da ya gabata ba, da kuma Sanatan jihar South Corolina Lindsey Graham da ya saba sukar shugaban kasar sun kare Trump a zaman shari'ar da aka yi.

    Amma ficen da shugaban kasar ya yi ba wai yana nufin cewa ba a ganin baiken shi a kan tuhume-tuhemen da aka yi masa ba, domin wata kuri'ar jin ra'ayi da aka yi ta nuna cewa kaso 54 cikin 100 na 'yan Republican ne ke da ra'ayin cewa shugaban bai aikata laifin komai ba.

    Yayin da sauran ke da ra'ayin cewa ba shakka ya tafka kuskure, amma bai kai a sauke shi daga mukaminsa ba.

    Senators voting in the US Senate
    AFP
    Yawan da ya wuce misali

    • 53Sanatocin Republican

      'Yan jam'iyyar Republican na da rinjaye a majalisar dattawa, domin suna da sanatoci 54 yayin da 'yan Democrat ke da 47, abin da ke nuna cewa su ne ke da rinjaye kuma suke da damar tsara yadda suke son shari'ar ta kasance.

      A yayin zaman, an jefa kuri'a kan bai wa karin shaidu damar bayyana, inda aka yi watsi da bukatar.

      Daya daga cikin sanatocin Republican Sanata Mitt Romney daga jihar Utah ya zabi a sauke shugaban ba tare da la'akari da cewa jam'iyyarsu daya ba, inda ya ce ya fi son ya kafa wa kansa tarihin da ba za a manta da shi ba.

      Reuters
      Yawan sanatocin da ake bukata don tsige shi

      • 67cikin sanatoci 100

        Wannan ne abin da yasa aka wanke shugaban, dama kuma tunanin da akai ta yi kenan, cewa majalisar za ta wanke shi domin dole sai an samu kashi biyu cikin uku na 'yan majalisar da za su amince da bukatar sauke shin, ma'ana sanatoci 67.

        Kenan dole sai sanatocin Republican 20 sun amince da bukatar 'yan Democrat kafin hakan ta kasance.

        Trump at a rally
        Getty Images
        Garabasar tsigewa?

        • dala miliyan 46da aka samu cikin watanni ukun da suka wuce

          Bayanai: Kungiyar Kamfe ta Trump

          Amurkawa sun yi ta aikawa asusun yakin neman zaben shugaban kasar makudan kudade domin taimaka wa aniyarsa ta zarcewa a kan mulki, wannan ya nuna cewa wasu 'yan kasar ba sa goyon bayan hakan.

          Yanzu shugaban na da damar maida hankalin sa akan yakin neman zabensa, ko da yake dama a kashin gaskiya kokarin tsige shin bai taba hana shi gudanar da kamfe ba.

          Shin tsige shin ya janyo masa bakin jini a idon Amurikawa ne ko kuwa soyayyar shi ce ma ta kara shiga zuciyarsu?

          Za mu san hakan nan da watanni uku masu zuwa.