Mutum biyar sun mutu a harin masallacin Gwoza

An wallafa
Mutane biyar sun rasu sakamakon harin da aka kai a wani masallaci da ke garin Gwoza a jihar Borno.
Lamarin ya auku ne a ranar Lahadi da asuba, kuma 'yan kunar bakin wake mata biyu da wasu mutanen uku ne suka rasu.
Haka kuma akwai wasu mutane tara da suka ji raunuka kuma suna can suna karbar magani a asibiti.
Wani ma'aikacin agaji ne ya tabbatar wa BBC hakan inda ya ce kawo yanzu babu kungiyar da ta dauki alhakin kai harin.
Jihar Borno da wasu yankuna a arewa maso gabashin Najeriya na da matukar hadari saboda hare-haren 'yan Boko Haram.

Asalin hoton, Getty Images





