Hotunan yadda shirin tsige Trump ke tayar da kura a Amurka

Asalin hoton, Getty Images
Masu zanga-zanga da ke neman a tsige shugaban Amurka Donald Trump sun taru a Capitol, a ranar Larabar 18 ga watan Disamban 2019, gabanin zaman majalisar wakilan kasar.
A ranar ne majalisar za ta kada kuri'a kan batun tsige shugaban.
Majalisar na zargin Trump da manyan laifuka biyu. Ingiza Ukraine ta fara bincike a kan tsohon mataimakin shugaban kasar Joe Bidnen.
Zargi na biyu kuma shi ne kin bai wa majalisar hadin kai a bincikenta a kan lamarin.

Asalin hoton, Getty Images
Wata mata mai goyon bayan Shugaba Donald Trump a kusa da Capitol a birnin Washinton, DC, gabanin 'yan majalisar wakilan kasar su kada kuri'ar tsige shugaban.
Majalisar na zargin Trump da kawo tarnaki a binciken da ake a kansa da kuma wuce gona da iri.

Asalin hoton, Getty Images
Magoyin bayan tsige Trump sanye da kayan Father Christmas dauke da jerin sunan Trump da mataimakinsa Mike Pence da wasu manyan jami'an gwamnatin shugaban da yake neman a tsige a matsayin kyautar kirsimetin bana.

Asalin hoton, Drew Angerer
Shugabar Majalisar Wakilan Amurka, Nancy Pelosy na tafiya zuwa ofishinta bayan isarta Capitol, a ranar 18 ga watan Disamba a birnin Washington.
A ranar ce majalisar za ta yi kuri'ar batun tsige Shugaba Donald Trump.

Asalin hoton, Drew Angerer

Asalin hoton, Getty Images
Tom McClain magoyin bayan Trump sanye kayan Father Christmas, yana wuce wasu masu zanga-zangar neman tsige shugaban na Amurka.

Asalin hoton, Getty Images
Taron masu zanga-zagnar neman majalisar Amurka ta tsige shugaban kasar Donald Trump saboda zargin da ake masa. Suna cewa a tsige shi don kare dimokradiyyar kasar.

Asalin hoton, Getty Images
Wasu mata na yin macin neman tsige Donald Trump saboda zargin aikata wasu laifuka.

Asalin hoton, Drew Angerer
Wasu magoya bayan Trump na daga tutar goyon bayan shugaba wanda majalisar wakilan kasar ke neman tsigewa.

Asalin hoton, Getty Images
Zanga-zangar mai taken 'Babu wanda ya fi karfin doka', na masu neman kawo karshen gwamnatin Trump a dandalin Times Square na birnin New York.

Asalin hoton, Drew Angerer
Masu goyon bayan Trump dauke da kwalin neman a tsige shugaban majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosy.

Asalin hoton, Getty Images











