Kan Amurkawa ya rabu kan tsige Donald Trump

An zargi Mr Trump da fifita bukatunsa a kan na kasa
Bayanan hoto, An zargi Mr Trump da fifita bukatunsa a kan na kasa
An wallafa

'Yan majalisar dokokin Amurka na shirin jefa kuri'ar tsige shugaba Donald Trump idan anjima a yau Laraba.

Hakan ya biyo bayan kammala binciken cewa ya aikata laifin da ke barazana ga tsaron kasar, da kuma fifita bukatun kansa a kan na al'ummar Amurka.

Wayar tarhon da shugaban ya yi da takwaransa na Ukraine, inda ya nemi da a binciki ayyukan da abokin takararsa na jam'iyyar Dimokrats Joe Biden ke yi a Ukraine din kafin Amurka ta aminta da bai wa kasar tallafin da ta saba.

Shugaba Donald Trump na Amurka ya bayyana shirin tsige shi da 'yan demokrats ke yi a matsayin juyin mulki.

A wata wasika da ya aike wa kakakin majalisar dokoki Nancy Pelosi, shugaban ya danganta abin da ake so ayi masa a matsayin wani abu da zai haifar da babbar matsala da kuma ke tattare da hatsari.

Mr Trump ya ce yin amfani da maganar da aka jiyo ta wayar tarho a matsayin wata kwakkwarar shaida bayan an tabbatar da cewa shugaban kasar Ukraine da shi ba su fadi wani mugun abu ba, ya nuna irin yadda "ake so a tsige ni ne ko ta halin 'ka'ka."

Batun tsige Donald Trump ya haifar da rikici a majalisar wakilai da 'yan Dimokrats ke da rinjaye da kuma ta dattijai da ,yan Republican ke jagoranta.

Trump

Kungiyoyin masu zanga-zanga da ke nuna adawa da tsige Mista Trump sun gudanar da zanga-zanga a biranen kasar da dama, inda da dama suka rike alamun da ke cewa "Ku tube Trump" da kuma tambarin Twitter na tsigewa - #ImpeachNow.

Wata kuri'ar jin ra'ayin mutane ta nuna kan 'yan kasar ya rabu biyu dangane da batun tsigewar.

Wani shafin intanet na siyasa na Amurka ya nuna cewa kaso 47 na Amurkawa na son a tsige Trump, inda kuma FiveThirtyEight's collection of national polls shows just over 47% back impeachment, while 46.4% do not support it.