'Abinci ya yi tsada saboda rufe iyakokin Najeriya'

Asalin hoton, Nigeria Government
Ministar Kudi ta Najeriya Zainab Ahmed Shamsuna ta ce rufe iyakokin Najeriya ya jawo tashin farashin kayayyaki a kasar.
Kalaman nata na zuwa ne yayin da rahoton Hukumar Kididdiga ta Najeriya ya ce tashin farashin kayayyaki ya kai kashi 11.61% a watan Oktoba.
Ministar ta fadi hakan ne ranar Laraba, inda ta ce wannan alkaluma da hukumar ta fitar suna sane da su tun a watan Satumba.
"Hauhawar farashin kaya ya sauko a cikin 'yan watanni amma ya ci gaba hawa a wata biyu da suka gabata, inda yanzu ya kai kashi 11.61% a karshen watan Oktoba," in ji a Zainab Shamsuna.
Ta ci gaba da cewa: "Hauhawar da aka samu tsakanin Satumba zuwa Oktoba ya faru ne saboda tsadar kayan abinci da kayan kanti da kuma kifi.
"Daya daga cikin dalilan da ya jawo hakan shi ne rufe iyakoki. Rufewar ta dan wani lokaci ce sannan kuma karin da aka samu na kashi biyu ne kawai (a kan na baya).
"Najeriya tana tattaunawa da makwabtanta kan batun kuma tattaunawar ta yi nisa."
Ministar kudin kuma ta ce burin gwamnati shi ne ta kare tattalin arzikin kasa daga durkushewa idan yarjejeniyar kasuwanci tsakanin kasashen Afirka maras shinge ta fara aiki.
Najeriya dai ta saka hannu kan yarjejeniyar tun a watan Yulin 2019, wadda ta tanadi shigar da kayayyaki na kasuwanci a tsakanin kasashen Afirka ba tare da shamaki ba.










