Dubban tsuntsaye sun mutu kusa da tafki a Indiya

Asalin hoton, Vikas Choudhary/Down to Earth
Wani babban jami'in kula da gandun daji a Indiya ya shaida wa BBC cewa an gano fiye da tsuntsaye 1,000 da suka mutu a gabar tafki mafi girma na kasar.
An gano tsuntsayen ne a kusa da Tafkin Sambhar mai nisan kilomita 80 daga kudu maso yammacin birnin Jaipur, a jihar Rajasthan da ke arewacin kasar.
Tsuntsayen dai na dangogi daban-daban ne da suka hada da wadanda ke yin kaura zuwa tafkin a duk shekara.
Hukumomin gwamnati na bincike kan abin da ya yi sanadin mutuwar tasu.
Wani babban jami'in kula da gandun daji Sanjay Kaushik ya ce, "Har yanzu muna kirga matattun tsuntsayen. Mushensu na nan birjik a kusa da tafkin. Sannan kuma ana kula da wasu 20 zuwa 25 da ba su mutu ba."
A ranar Lahadi ne aka fara samun rahotannin mutuwar tsuntsayen, a lokacin da masu yawon bude ido da ke ziyara kusa da tafkin suka gansu.
"Ba mu taba ganin abu makamancin wannan ba," a cewar Abhinav Vaishnav, wani mai tu'ammali da tsuntsaye a yankin, kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Indiya.

Asalin hoton, Vikas Choudhary/Down To Earth
Wani mai daukar hoto Vikas Choudhary, ya ce mushen tsuntsayen na nan birjik inda suka cika kusa tsawon kilomita 12 na yankin.
"Na tabbata yawan wadanda suka mutun zai karu, wata kila ma su kai 5,000. Ba abin da ka ke gani a wajen sai mushen tsuntsaye," in ji Mr Choudhary a lokacin da yake gaya wa BBC.
An binne mushen tsuntsayen a wani katon rami da aka tona kusa da tafkin.
Jami'in kula da gandun daji Rajendra Jakhar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Indiya cewa wata kila ruwa da kankara mai karfi da aka yi a yankin kwanaki kadan da suka gabata ne, suka jawo mutuwar tasu.

Asalin hoton, Vikas Choudhary/Down To Earth
"Muna kuma duba yiwuwar wata kila gurbacewar ruwa ne ko yaduwar kwayoyin cuta suka jawo," a cewarsa.
Wani likitan dabbobi na yankin kuma ya ce mai yiwuwa murar tsuntsaye ce ta yi ajalinsu.
Tuni dai aka aika wasu tsuntsaye dakin gwaje-gwaje da Bhopal don gano sanadin.












