Ghana: Mataimakin shugaban kasa zai kai yaran Fulani karatun likita

Wani yaro Bafulatani tare da shanunsa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A baya dai Fulani sun fuskanci wariya a kasar Ghana
An wallafa

Matar mataimakin shugaban kasar Ghana Hajiya Samira Bawumia, ta sanar da wani shirin daukar nauyin 'ya'yan Fulani zuwa kasar Cuba domin yin karatun aikin likita.

Hajiya Samira ta ce mijinta Mahamudu Bawumia ne ya umarce ta da ta yi hakan karkashin wani shiri na daukar nauyin daliban Zango, cikinsu har da Fulani.

Ta bayyana hakan ne a wurin taron kasa na kungiyar Fulani ta Tabital Pulaku, wanda aka gudanar a birnin Tamale.

Alhaji Yakubu Bari shi ne shugaban kungiyar ta kasar Ghana, kuma ya shaida wa wakilin BBC Fahad Adam cewa zuwa yanzu dai ba a bayyana adadin yaran da za a bai wa wannan tallafin karatu ba.

Sannan ya bayyana su ne za su mika takardun duk mai sha'awar cin gajiyar shirin ga ofishin mataimakin shugaban kasar.

"Ba ta fadi adadi ba amma daga maganarta muna fatan za ta taimaka wa yara da yawa," in ji Yakubu Bari.

A shekarar 2015 al'ummar Fulani sun fuskanci matsalolin kyama a Ghana, inda aka yi masu korar kare daga jihar Volta.

Hakan ya sa kungiyar Tabital Pulaku ta yi barazanar kai gwamantin kasar gaban kotun Kungiyar Tarayyar Afirka ta AU da kuma ta Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka wato ECOWAS.

Sai dai Alhaji Yakubu Bari ya aminta cewa Fulani na daga cikin koma-baya a bangaren ilimin zamani a Ghana.

"Fulanawanmu (Fulaninmu) sun mayar da kansu baya kadan a bangaren karatun boko amma mun gano cewa wannan rashin karatu yana kawo mana matsala kwarai.

"Muna kiran iyaye maza da mata muna fadakar da su cewa su saka himma wajen saka yaransu a makaranta domin su samu ilimin boko.

"Muna zuwa kauyukansu muna yi masu nasiha cewa idan ba ka da ilimi to kamar makaho ne kai a cikin duniyar nan."