EFCC ta yi wawan kamu a jihar Kwara

Magu

Asalin hoton, Others

Bayanan hoto, Mukaddashin Shugaban Hukumar EFCC Ibrahim Magu
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon-kasa a Najeriya, wato EFCC ta kama wasu shugabannin kananan hukumomi 16 na jihar Kwara, bisa zarginsu da yin facaka da wani bangaren kudin gwamnati da ya kai naira biliyan hudu.

A halin da ake ciki dai wadanda ake zargin suna amsa tambayoyi a hannun hukumar.

Shugabannin kananan hukumomin 16, wadanda hukumar ta kama, watakila su yi hutun karshen mako a caji-ofis din hukumar, sakamakon bincike da jami`anta ke musu.

Ana zargin sun sa-hannu sun zari wani kudi da ya kai naira miliyan 100 daga cikin wani kudi da suka hada-gwiwar majalisun kananan hukumomin nasu suka karbi rancen naira biliyon hudu daga bankin Sterling.

Rahotannin sun ce sun karbi kudin ne don biyan albashi da wasu hakkokin malaman makaranta da ke karkashin shirin nan na ba da ilimi kyauta, wato UBEC.

Duk da cewa shugabannin kananan hukumomin da ake zargi an ce sun dan ciri naira miliyan 100 ne daga cikin kudin da sunan rance, bincike ya nuna babu wata dokar da ta ba su damar zara.

Kazalika ana zargin su da yin sama-da-fadi da wani bangare na kudin-shigar kananan hukumomin da suka mulka.

Kasancewar suna karkatar da kashi 10 cikin 100 na kudaden da akan tattara daga rumfunan kasuwanni da sauran kafofi na cikin gida, zuwa cikin asussansu na banki kai-tsaye, lamarin da ya saba da ka`idojin sarrafa kudi na gwamnati.

Hukumar EFCC ta tabbatar da kama shugabannin kananan hukumomin a shafinta na Twitter, amma ba ta yi bayani dalla a kan abin da ta bankado ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Ba ta kuma yi bayani a kan tsawon lokacin da za su kawshe a hannunta ba.

Su ma wadanda ake zargin, babu wani cikakken bayanin da ya fito kai-tsaye daga waninsu dangane da zargin da ake musu.

Kodayake wata majiya na cewa suna kokarin daidaitawa da hukumar EFCC, ko za ta ba su damar biyan kudin da ake zargin sun murshe.

A watan Yunin da ya wuce aka dakatar da shugabannin kananan hukumomin daga mukamansu bisa zargin facaka da kudin gwamnati, bayan majalisar dokokin jihar ta bai wa Gwamna Abdulrahman Abdulrazak damar yin haka, har ma a lokacin shugabannin kananan hukumomin suka gurfanar da gwamnan a gaban kuliya.