Aikin lauya: Daliban Ghana sun yi zargin manakisa

Zanga-zangar daliban Ghana kan faduwa kashi 97 a jarabawar shiga makarantar aikin lauya
Bayanan hoto, Zanga-zangar daliban Ghana kan faduwar kashi 97 a jarabawar shiga makarantar aikin lauya
An wallafa

Dalibai sun yi zanga-zanga bayan kashi 97 na takwarorinsu sun fadi jarabawar shiga makarantar koyon aikin lauya a Accra babban birnin kasar Ghana.

Mutane 128 ne daga cikin dalibai 1,820 suka ci jarabawar shiga makarantar aikin lauyan ta 2019 a Ghana. Adadin shi ne kashi 97 na wadandan suka rubuta jarabawar.

Masu zanga-zangar na zargin cewa faduwar kashi 97 na wadanda suka rubuta jarabawar kokari ne na ganin manyan mutanen sun yi kaka gidan aikin lauya a kasar.

Suna zargin yawan faduwar jarabawar a matsayin kokarin mayar da marasa karfi saniyar ware a aikin lauya domin manyan mutane.

"Sun sauya tsarin. Dole a daina wannan abin da suke yi na mayar da Makarantar Aikin Lauya ta Ghana ta koma ta 'yan uwa da dangin manyan mutane," a cewar wani daga cikin masu zanga-zangar.

A baya babban alkalin Ghana, Sophia Akuffo, ya bayyana rashin amincewarsa ga yawaitan lauyoyi a kasar wanda ya ce na kawo nakasu ga nagartar aikin.

Masu zanga-zangar sun bukaci shugaba Nana Akufo-Addo ya sanya baki ya kawo gyara a matsalar da suka ce "abin kunya" ne.