'Mutane 60 sun mutu yayin zanga-zanga a Iraki'

Asalin hoton, AFP
Jami'an gwamnatin Iraki sun ce zuwa yanzu a kalla mutum 60 ne aka tabbatar sun mutu a yayin zanga-zangar kin jinin gwamnati ta kwana hudu, a fadin kasar.
An kuma bayyana cewa an raunata wasu daruruwa. Yawancin wadanda suka mutun sun rasa rayukansu ne a ranar Juma'a, ciki har da a kalla 'yan sanda biyu.
Wannan rikici dai ya kasance daya daga cikin mafiya muni da aka gani a kasar tun bayan murkushe masu tayar da kayar baya na kungiyar IS shekaru biyu da suka wuce.
Zanga- zangar ta fara ne domin nuna rashin jin dadi da jama'a ke yi a kan rashawa da kuma rashin aikin yi, to amma yanzu kuma yawancin masu zanga-zangar na neman gwamnati ta sauka ne.
Malamin Shi'ar nan mai karfin fada a ji a kasar, Moqtada al Sadr, shi ma ya yi kira ga Firaministan Iraqin da ya sauka daga mukaminsa, a kuma yi zabe na gaggawa.
Haka shi ma babban malamin Shi'a na kasar, Ayatollah Ali al-Sistani ya yi Allah-wadai da tashin hankalin da jami'an tsaro da masu zanga-zangar ke yi a fadin kasar.
Da yake jawabi a wata huduba a Karbala, kakakin malamin, Ahmed al-Safi, ya ce gwamnati ta gaza amsa bukatar sauyin da mutane ke raji, kuma ya kamata ta dauki mataki kafin lokaci ya kure mata:
Ya ce, ''Mai alfarma, Sistani ya gargadi wadanda suke taka birki ga guguwar sauyin, suke kuma ganin cewa rajin sauyin zai lafa, to su sani cewa shi fa sauyi abu ne da ba shi da makawa.''
Duk da zubar da jinin da ake yi, gwamnati ta bayar da umarnin dage dokar hana zirga-zirga a Bagadaza daga asuba a ranar Asabar, sai dai ba a sani ba ko za a dage dokar ma a sauran biranen Iraki.











