Za a fatattaki 'yan gudun hijira daga Italiya

Asalin hoton, ENCARNI PINDADO
Ministan harkokin wajen Italiya Luigi Di Maio, ya ce za a fitar da dukkan masu neman mafaka wadanda ba su cancanci zama a kasar ba a cikin wata hudu.
Sanarwar na daga wani muhimmin mataki na gwamnatin kasar ta Italiya na magance matsalar tururuwar 'yan gudun hijira, wadanda yawancinsu daga Afirka da kuma Gabas ta Tsakiya suke.
Mr di Maio ya ce matakin na hanzarta fitar da 'yan gudun hijirar da 'yan ci-rani daga Italiyar, ta hakan gwamnatin kasar na aikawa da kwakkwaran sako ga masu neman mafaka na bogi.
Haka kuma ya fitar da sabon jerin sunayen kasashen da ake ganin babu wata matsala ko hadari a tura 'yan gudun hijira can.
Kasashen sun hada da Algeria da Morocco da Tunisia da Senegal.
Ministan harkokin wajen na Italiya ya ce ba ya ganin dabarar rarraba 'yan gudun hijira ko 'yan ci-rani a tsakanin kasashen Tarayyar Turai shi ne mafita.
Ya ce, '' Ban yarda cewa rarraba 'yan gudun hijirar a sauran kasashen Turai ba ita ce tabbatacciyar mafita ba. Rarrabasun kawai na taimaka mana ne kawai mu magance matsalar 'yan gudun hijirar a matsayin mu na Turai, amma ba a matsayin Italiya ba.''
Za a bi sabbin matakan ne da wasu yarjeniyoyi da kasashen Afirka wadanda daga nan ne yawancin 'yan gudun hijira ko 'yan ci-rani ke tashi daga cikinsu domin zuwa Turai, ta tashoshin ruwa na Libya.
Mista Di Maio ya ce tare hanyoyin da ake bi ana kokarin shiga Turan zai taimaka wajen magance matsalar.











