Cin hanci na kara kamari a Jamhuriyyar Nijar - IMF

Asalin hoton, Getty Images
Wani rahoton da ssusun bayar da lamuni na duniya IMF, ya fitar ya bayyana cewa matsalar cin hanci na yin tarnaki ga ci gaban Jamhuriyar Nijar.
Rahoton dai ya lissafa wasu hukumomi da ma'aikatun gwamnati inda matsalar ta fi yin kamari.
IMF ya ce matsalar cin hanci na kan gaba wajen hana ruwa gudu a Nijar.
Cin hancin da karbar rashawa sun yi kaka gida a wasu fannoni da rahoton ya ambato irin su ma'aikatar kwastam da 'yan sanda da ma'aikatar bayar da kwangiloli ta gwamnati da kuma ma'aikatar haraji.
Sai dai rahoton ya ce kungiyoyin siyasa da ma na fararen hula da kuma sarakunan gargajiya ma suna taka muhimmiyar rawa a batun cin rashawa.
Mamman Wada na kungiyar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta Transparency International, ya ce siyasantar da ma'aikatun gwamnati da kin daukar doka a hannu, da gazawar fannin shari'a na daga cikin dalilan da suka sa cin hancin ke kara bazuwa a kasar.
Ya ce dole gwamnati ta kara kaimi kan kokarin da take yi wajen yaki da wannan matsala.







