Xenphobia: Najeriya ta kaurace wa taron tattalin arziki a Afirka Ta Kudu

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Najeriya ta kaurace wa taron tattalin arziki na duniya wato World Ecomnic Forum wanda ake farawa a ranar Laraba a birnin Cape Town na kasar Afirka Ta Kudu.
Wannan ya biyo bayan hare-haren da 'yan kasar suke kai wa baki 'yan kasashen waje, wadanda da yawa daga cikin wadanda abin ya shafa 'yan Najeriya ne.
Taron dai na kwana biyu ne, wanda ake budewa a yau Laraba har zuwa Juma'a kuma Najeriya na daga cikin kasashen da za su halarta.
A wani sako da Bashir Ahmad mai bai wa Shugaban Kasa shawara kan kafafen sada zumunta ya wallafa a Twitter, ya ce gwamnati ta kaurace wa taron amma wasu daga cikin 'yan Najeriya na halarta bisa radin kansu.
Tun farko dai wani ne mai suna @Ayourb ya wallafa kokwantonsa a Twitter cewa ya ji Najeriya ta janye daga halartar taron amma yana kokarin ya tabbatar da gaskiyar labarin.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Sai Bashir Ahmad din ya mayar masa da martani cewa:
"Eh gaskiya ne gwamnatin Najeriya ta kaurace wa taron tattalin arziki na World Economic Forum da ake yi a Cape Town na Afirka Ta Kudu.
'Duk wadanda kuma suka je daga Najeriya, ciki har da wani tsohon minista, sun je ne bisa radin kansu."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Rikici ya barke a dare na biyu a unguwar Alexander a birnin Johannesburg inda daruruwan mutane suka yi tattaki a tituna ranar 2 ga watan satumba a wani mataki da ba a saba ganin irinsa ba na nuna tsananin kin jinin baki.
Wane hali 'yan kasashen waje ke ciki a Afirka ta Kudu?

Asalin hoton, Getty Images
A kan wannan al'amari, BBC ta tuntubi wani dan Najeriya mazaunin birnin Johanasbag na Afirka ta Kudun.
Mutumin mai suna Ibrahim Bitrus ya bayyana halin da 'yan kasashen waje ke ciki yanzu, a wata hira da yayi da BBC:
"Rikicin ya samo asali ne a lokaicn da wani dan kasar Tanzaniya ya tafi wata unguwa domin sayar da wasu kwayoyi masu sa maye."
Ya ce, "Kwayoyi ne da matasa kan nuka, su saka cikin taba suna sha. To wasu direbobin motocin tasi a unguwar sun hana yaron zuwa unguwar, amma ya ki".
"To da suka kama shi ne sai suka dake shi. Shi kuma sai ya tafi gida ya dauko bindiga ya harbi wani daga cikin wadanda suka doke shi", in ji Ibrahim Bitrus.

Asalin hoton, Getty Images
Ya kuma bayyana wa BBC cewa a sanadin haka ne aka dora wa 'yan Najeriya wannan laifin, kuma daga nan aka fara kai musu hare-hare.
Ya kuma ce wutar rikicin ta fara ne daga babban birnin kasar Pretoria, kafin daga baya ta bazu zuwa birnin Johannesburg.










