Karuwar laifuka a Barcelona na dakile yawon bude ido

Sane babbar matsala ce Las Ramblas - wani babban wurin yawan bude ido.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An samu karin yawaitar laifuka da kashi 9 cikin 100 a wata shida na farkon a wannan shekara idan aka kwatanta da shekarar 2018
    • Marubuci, Daga Guy Hedgecoe
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Madrid
  • An wallafa

Rikici sosai har da shake wani jakada ya yi karin haske a kan karuwar laifuka a birnin Barcelona, abin da ke bai wa mutanen wurin da mahukunta tsoro.

Jakadan kasar Afghanistan da ke kasar Spaniya, Masood Khalili, an far masa da makami inda aka kada shi a ranar Lahadi da dare bayan an sace masa agogo.

A wasu gidaje da ke kusa a ranar Lahadi da dare, wata Bafaranshiya mai shekara 91 ta samu rauni a kanta a lokacin da barayi suka kama sarkar da ke wuyanta.

Wani dan yawan bude ido an masa aiki a asibiti bayan an yi masa fashi a wata unguwa kwanaki biyu da suka wuce.

Shugaban jami'an tsaro na garin Barcelona, Albert Batlle, ya musanta abin da ke faruwa a matsayin wani "babban rikici" alkaluma sun nuna cewa abin ya fara ne gadan-gadan kafin lokacin bazara.

An samu karin yawaitar laifuka da kashi 9 cikin 100 a wata shida na farkon a wannan shekara idan aka kwatanta da shekarar 2018.

Manyan laifuka sun yi sama da kashi 31 cikin 100 a wannan lokacin, wanda a cikin shekara uku ya tashi da kashi 60 cikin 100, fashi kuma ya tashi da kaso 66 cikin 100.

"Lokaci ya yi da zama aminta cewa abin ya fi karfinmu" a cewar Luis Sans, shugaban 'yan kasuwan Passeig de Gràcia.

Gwamnatin yankin Catalonia ta amince za ta sanya 'yan sanda domin sintiri a kan tituna.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Gwamnatin yankin Catalonia ta amince za ta sanya 'yan sanda domin sintiri a kan tituna

Birnin mai yawan mutane miliyan 1.6, ya samu masu yawan bude ido miliyan 16 a shekarar da ta gabata.

'Yan sane na yawaitar ziyarar wuraren da masu yawon bude ido suke zuwa kamar su Ramblas boulevard da kuma Ciutat Vella.