Ba zan sake murna ba - angon da aka tayar da bam a bikinsa

Mirwais Elmi a yayin da ya ke magana da kafar yada labarai ta Tolo News

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Mirwais Elmi ya gayyawa kafar yada labarai ta Tolo News cewa ba zai sake murna a rayuwarsa ba
An wallafa

Wani ango da ya fuskanci tashin bam a yayin bikinsa a birnin Kabul na Afghanistan ya ce ba shi da sauran kwarin gwiwa bayan mummunan harin.

A cikin wata hira ta gidan talabijin, Mirwais Elmi ya bayyana cewa amaryarsa ta tsira amma sauran 'yan uwansa na cikin mutum 63 da suka rasa rayukansu a harin da aka kai ranar Asabar.

Kungiyar mayakan IS sun dauki alhakin kai harin, wanda ya raunata fiye da mutum 180.

Shugaba Ashraf Ghani dai ya yi Allah-wadai da kai harin, yana mai cewa "dabbanci ne".

Ya zargi kungiyar Taliban da "bude wa 'yan ta'adda hanya".

Taliban, wacce a yanzu ke gudanar da zaman tattaunawa na neman sulhu da Amurka ta soki harin.

A cikin hirar da ya yi da Tolo News, Mirwais Elmi ya ce ya tuna yadda ya rinka gaisawa da bakin da suka cika dakin taron bikin nasa makil, cikin annashuwa, amma kwatsam bayan 'yan sa'o'i sai aka rinka fitar da gawarwakinsu.

Janaiza a birnin Kabul na Afghanistan August 18, 2019

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, An yi jana'izar yawancin mutanen da harin ya rutsa da su

"Amaryata da 'yan uwana duk suna cikin dimuwa, ba za su iya magana ba ma. Amaryar tawa ma sai suma take yi," a cewarsa.

"Ba ni da saurin kwarin gwiwa. Na rasa kani na, na rasa abokai na. Ba zan taba samun farin ciki a rayuwata ba.

Tattaunawar zaman lafiya

Ya kara da cewa: "Ba zan iya halartar jana'izarsu ba, ba ni da karfin zuwa... Na dai san wannan ba shi ne karo na karshe da 'yan Afghanistan za su sha wuya ba, za a ci gaba da shan wahala".

Mahaifin amaryar ya bayyana wa kafafen yada labarai na Afghanistan cewa 'yan uwansa 14 ne suka rasa rayukansu a yayin harin.

Dukda cewa ana tattaunwa domin ganin yadda za a kawo karshen yakin da aka shafe shekara 18 ana yi da Amurka, fararen hula a Afghanistan suna ci gaba da shan wahala a yanzu.

Wannan sabon harin da aka kai na nuna yadda za a sha wuya kafin a samu zaman lafiya a Afghanistan.

IS wacce ke da karfi a arewaci da kuma gabashin Afghanistan, kuma wacce ke yaki da gwamnati da kuma kawancen Amurka ba ta cikin tattaunawar da ake yi ta samar da zaman lafiya.

Taliban dai tana iko da yankuna da dama a kasar, wadanda ba ta samu ikon yin hakan ba tun bayan da aka hambarar da ita daga kan mulki a shekarar 2001.