Turkiyya za ta kaddamar da farmaki a Siriya

Asalin hoton, AFP
Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, ya bayyana cewa kasarsa za ta kaddamar da farmakin soji kan dakarun Kurdawa da ke samun goyon bayan Amurka a arewacin Siriya.
Ya ce farmakin zai mayar da hankali kan yankunan da dakarun na YPG ke iko da su agabashin kogin Euphrates.
A baya ma Turkiyya ta kaddamar da farmaki kan mayakan na Kurdawa.
Za a iya cewa dakarun na YPG sun kafa wani kwarya-kwaryar yanki mai cin gashin kansa a gabashin kogin na Euphrates a arewacin Siriya.
Hakan dai ya basu damar taka muhimmiyar rawa a nasarar da aka samu wurin fatattakar mayakan kungiyar IS, inda suke tsallakawa daya bangaren kogin suna kwace iko da garuruwan IS din.
A baya Turkiyya ta kaddamar da makamancin wannan farmaki domin korar mayakan na Kurdawa daga wannan yankin - tana kallonsu a matsayin kungiyar 'yan ta'adda.
Sai dai goyon bayan da Amurka ke ba su ya sa ta a tsaka mai wuya.
A lokacin da Amurka ke shirin yanje inata-inata daga Siriya, ta yi alkawarin samar da wani tudun muntsira a arewacin Siriya da ke da iyaka da Turkiyya.
Sai dai daga dukkan alamu Turkiyya ta gaji da jan kafar da Amurkan ke yi na yin hakan.
Ana ganin kaddamar da yaki kan Kurdawan a yankin ka iya haifar da wani kazamin fada na daban.










