Yadda gini ya rufto ya kashe mutum 11 a Jos

Lagos

Asalin hoton, LASEMA

Bayanan hoto, Za a ci gaba da ayyukan ceto a ranar Talata don fito da sauran wadanda baraguzai ya danne
An wallafa

Kungiyar agaji ta Red Cross a Najeriya ta ce an zakulo karin gawawwakin mutane hudu a baraguzan wani ginin da ya rufta a Jos babban birnin jihar Filato, abin da ya sanya adadin wadanda suka mutu ya kai 11.

A yammacin ranar Litinin ne dai ginin wanda ya kunshi kantuna da kuma wuraren zaman jama'a ya rufta, abin da ya haifar da asarar dukiya da rayuka.

Duk da cewa har yanzu ba a san abin da ya jawo faduwar ginin ba, 'yan sanda sun ce sun aika tawagar su ta masu aikin ceto zuwa wajen don taimakawa wadanda abin ya rutsa da su.

Jami'in yada labaran 'yan sanda a jihar ta Filato, DSP Tyopev Mathias ya ce da misalin karfe hudu na yammacin Litinin ne aka kira su don sanar da su abin da ya faru, kuma ba su bata lokaci ba don zuwa wajen, inda suka ceto mutum bakwai da ba su ji rauni ba..

Daga bisani kuma masu aikin ceto suka sake fito da wasu mutanen da suka jikkata aka kai su asibitin Kwararru na Filato da kuma Asibitin Koyarwa na Jami'ar Bingham domin a duba su.

Wannan layi ne

Ayyukan ceton da ake yi

Masu aikin ceto da dama sun hallara a wajen tun yammacin da abin ya faru har zuwa tsakar dare domin kokarin ceto wadanda baraguzai ya danne.

Suna amfani da shebur da diga, wasu har da hannu don kawar da baraguzan.

Daruruwan mutanen da suka taru a wajen ma sun sanya hannu don taimakawa jami'ai.

Short presentational grey line

Yawan rushewar gini a Najeriya

Ana yawan samun rushewar gine-gine a Najeriya musamman a manyan biranen kasar Legas da Abuj da Fatakwal, abun da ke jawo asarar rayuka da dumbin dukiya.

Ko a wannan shekarar ta 2019 sau biyu gini yana ruftawa a Legas, sannan wani kuma ya rufta a Ibadan.

A shekarar 2014 kawai kusan sama da mutum 120 ne suka mutu sakamakon wannan iftila'in a Legas.

A watan Disambar shekarar 2016 ma wani ginin coci ya rushe a Legas din inda akalla mutum 116 suka rasa rayukansu.

Hakazalika a watan Maris din shekarar 2016, wani gini da ba a kammala gininsa ba ya rufta a gundumar Leki, inda mutum 34 suka mutu, aka ceto wasu 13 da ransu daga buraguzai.

An shafe kwana biyu ana aikin ceto a wancan lokacin.

A 2016 din dai kuma fiye da mutum 100 ne suka mutu bayan da wani ginin coci ya rufta a kansu a birnin Uyo da ke kudancin Najeriya.

Short presentational grey line

Matsalar rushewar gine-gine a Najeriya

Yawan rushewar gine-gine da ake samu a Najeriya cikin shekaru ashirin da suka gabata abun damuwa ne matuka, saboda yadda ake samun asarar rayuka da dukiya sakamakon hakan.

Masana sun bayyana abubuwa da dama a matsayin wadanda ke jawo rushewar gine-ginen da suka hada da aikace-aikacen dan adam da ko kuma wata kaddara daga Ubangiji.

Hakan yana da matukar illa ga al'umma da kuma zuba jari a bangaren gine-gine.

Abubuwan da ke jawo rushewar gini

  • Kayan gini marasa inganci
  • Rashin aiki mai kyau
  • Rashin saka tubali mai kyau
  • Rashin amfani da kwararru a harkar gini
  • Cin hanci da ya dabaibaye bangaren gine-gine
  • Rashin bin ka'idojin da dokokin gine-gine
  • Rashin kula
  • Rashin bin shawarar kwararu
  • Rashin tsara gini yadda ya kamata
  • Dora kaya fiye da kima
  • Mamakon ruwan sama
  • Saba ka'idojin gini na hukuma.