Ana fargabar mutum 80 sun nutse a teku sun mutu

Migrants are seen in a rubber dinghy as they are rescued by Libyan coast guards off the coast of Libya, 15 January 2015

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, 'Yan cirani kan tashi ne daga Libiya don kama hanyar Turai
An wallafa

Ana fargabar cewa 'yan cirani 80 ne suka mutu bayan da wani jirgin ruwa ya nutse da su a gabar tekun Tunusiya.

An tserar da mutum hudu daga cikin karamin kwale-kwalen - wanda ya nutse cikin teku kusa da garin Zarzis - amma daya daga cikinsu ya mutu a asibiti, kamar yadda rahotanni suka ce.

Mutane ukun da aka ceto din 'yan Mali ne kuma sun ce sun taso ne daga garin Zuwara na Libiya.

'Yan cirani kan tashi ne daga Libiya don kama hanyar Turai.

Yaki ya daidata Libiya tun 2011 lokacin da ake kokarin hambarar da Shugaba Muammar Gaddafi.

Dubban 'yan cirani wadanda da yawansu 'yan yankin Kudu da hamadar Sahara ne na tsare a sansanonin kasar daban-daban.

A ranar Laraba kuwa a kalla 'yan cirani 53 ne suka mutu, wadanda ke tsare a wani sansani a Tripoli bayan da wani harin sama ya shafi wajen.

Map of Libya and Tunisia

A watan Mayu ma a kalla mutum 65 ne suka nutse a gabar tekun Tunusiya bayan tasowar jirgin ruwansu daga gabar tekun Libiya.