Khalid Al Qasimi: Yarima daga UAE ya mutu a Landan

Asalin hoton, Getty Images
'Yan sandan birnin Landan na gudanar da bincike kan mutuwar da ba a iya fayyace sanadinta ba, ta wani yarima daga Gabas ta Tsakiya.
An samu yarima mai jiran gado kuma d'a ga basaraken Sharjah ta Hadaddiyar Daular Larabawa, Sheikh Khalid bin Sultan Al Qasimi, kwance rai ya yi halinsa shekaran jiya Litinin.
Sheikh Khalid Al Qasimi mai shekara 39 ya kafa kansa a sana'ar tsara dinkunan kwalisa kuma tufafin da ya dinka har sukan samu shiga baje-kolin tufafin 'yan birni na mako-mako a London.
Sai dai a ranar Litinin, d'an basaraken na Sharjah kwatsam ya fadi ya mutu.
'Yan sandan birnin Landan ko da yake ba su ambaci sunan yariman kai tsaye ba, amma sun ce an kira su wani gida a unguwar Knightsbridge da ke tsakiyar birnin inda suka samu gawar wani mutum da ya doshi shekara 40.
Binciken musabbabin rasuwar da aka yi masa bai kammala ba kuma 'yan sanda sun ce suna dakon sakamakon k'arin gwaje-gwaje.
Gwamnatin Sharjah ta ce a ranar Laraba za a binne mamacin, abin da ke nufin yiwuwar k'arin gwaje-gwajen sababin mutuwar ba lallai ba ne.
Babban wa ga Khalid Al Qasimi shi ma ya rasu ne a Burtaniya shekara 20 da ta wuce sakamakon shan kwaya fiye da kima. An dai ayyana makokin kwana uku a Daular Larabawa.
Tuni jama'a suka fara bayyana alhininsu a shafukan sada zumunta:
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a Instagram

Ambasadan Birtaniya a kasar, Patrick Moody, ya bayyana alhininsa ga iyalan yariman.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X












