Abin da ya faru a Afirka makon jiya

An wallafa

Zababbun hotunan abubuwan da suka faru a Afirka makon jiya

A woman at a rally in Abuja taking a selfie in Abuja, Nigeria - Tuesday 5 December 2017

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar Talata ne wata mata ta dauki hoton kanta lokacin da mata suka yi zanga-zanga kan bukatar a karfafa musu gwiwa ta hanyar sana'o'i a birnin Abuja da ke Najeriya
Fifi Loukoula taking part in the women's up to 67kg category in Mexico City, Mexico - Wednesday 6 December 2017

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Laraba ne Fifi Loukoula na Congo-Brazzaville ya samu kai wa zagaye na gaba a gasar daga karfe ta duniya da ake yi a Mexico
Cameroonian handball player Vanessa Djiepmou Medibe competing in Leipzig, Germany - Tuesday 5 December 2017

Asalin hoton, Empics

Bayanan hoto, A ranar Talata ne 'yar kwallon hannu ta Kamaru Vanessa Djiepmou ta yi nasara a Leipzig da ke kasar Jamus
A dancer at Blaise Diagne International Airport in Senegal - Thursday 7 December 2017

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Alhamis ne wata 'yar Senegal take rawa lokacin bikin bude sabon filin jirgin sama a babban birnin kasar Dakar
Sierra Leonean singer Janka Nabay at Le Liberte music hall in Rennes, Frances - Wednesday 6 December 2017

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Laraba ne aka daukin hoton mawaki dan kasar Saliyo Janka Nabay a dakin wake-wake na Le Libert a birnin Rennes da ke Faransa
People looking out of windows in Algiers, Algeria - Wednesday 6 December 2017

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Alhamis ne mutane suka leko kallon shugaban Faransa Emmanuel Macron
French President Emmanuel Macron is surrounded by security as he greets children in the streets of Algiers, Algeria- Wednesday 6 December 2017

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Emmanuel Macron ya kai ziyara karon farko yankin da suke neman 'yancin kai daga Faransa
Protesters burn a US flag in Tunis, Tunisia - Thursday 7 December 2017

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar Alhamis ne wadansu masu zanga-zanga suka kona tutar Amurka a Tunisiya
A migrant protests in opposition to the slavery of refugees in Athens, Greece - Saturday 2 December 2017

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A ranar Asabar ne 'yan ci rani suka yi zanga-zanga a kan rahoton da aka samu na sayar da su a matsatin bayi a kasar Libya
A woman plays with a child during the screening of 150 migrants brought home from Libya at the Murtala Mohammed International Airport in Lagos, Nigeria - Tuesday 5 December 2017

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Talata ne aka dauki hoton wata 'yar Najeriya bayan an dawo da ita gida a kokari da take na tsallakawa kasar Turai ta tsallakawa ta Libya
Children drawing in Juba, South Sudan - Tuesday 5 December 2017

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Talata ne wadansu yara suke zana hoton Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir a babban birnin kasar Juba
A portrait of Zimbabwe's new President Emmerson Mnangagwa is hung at State House, Harare, Zimbabwe - Monday 4 December 2017

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Litinin ne aka saka hoton Emmerson Mnangagwa a gidan gwamnatin Zimbabwe, bayan kwana 10 da rantsar da shi a matsayin shugaban kasa
A child walks through the hall of the derelict palace of Mobutu Sese Seko in Gbadolite, DR Congo - Sunday 3 December 2017

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Lahadi ne wani yaro yake kewayawa a cikin babban dakin fadar Mobutu Sese Seko tsohon Shugaban Zaire., inda yanzu ake kira Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo
A supermoon rises over Table Mountain in Cape Town, South Africa - Sunday 3 December 2017

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A ranar Lahadi ne farin wata ya haskaka wani tsauni a Afirka ta Kudu
An event organiser looking at a phone at Swahili Fashion Week in Dar es Salaam, Tanzania - Saturday 2 December 2017

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Asabar ne wata take duba wayarta a makon tallan kayan kawa na Swahili da aka yi a Dar es Salaam babban birnin Tanzaniya
A model pictured during Swahili Fashion Week in Dar es Salaam, Tanzania - Saturday 2 December 2017

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Asabar ne aka yi makon tallan kayan kawa na shekara-shekara da ake yi Dar es Salaam, babban birnin Tanzaniya
Male models with nose rings at Swahili Fashion Week in Dar es Salaam, Tanzania - Saturday 2 December 2017

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wasu maza masu tallan kayan kawa lokacin a lokacin makon kayan ado na Swahili a birnin Dar es Salaam
Queen Elizabeth II of the UK greets Nigeria's ambassador to the UK George Adesola Oguntade and his wife during a Modupe Oguntade during a private audience at Buckingham Palace in central London, UK - Wednesday 6 December 2017

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Sabon Jakadan Najeriya a kasar Birtaniya, George Adesola Oguntade, yayin da ya gabatar da takardar kama aiki ga Sarauniyar Ingila Elizabeth II a fadarta ranar Laraba